Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 05 16Article 450813

BBC Hausa of Sunday, 16 May 2021

Source: BBC

Citta tana saukaka cutar hawan jini da ciwon mara lokacin jinin ala'ada

Hoton citta Hoton citta

Citta wata nau'in saiwa ce da masana suka bayyana cewa ta samo asali ne daga yankin Kudancin Asia, kuma tana daga cikin kayan kamshi da ake amfani da su wajen dafe-dafen abinci ko kuma abin sha.

Ana kuma iya amfani da citta a danyar ta, ko busasshiya ko a garin ta har ma da ruwan ta, kuma tana da saukin samu a kasuwanni a fadin duniya.

A wasu lokutan akan hada ta da wasu sinadaran gyaran fatar jiki da kuma abinci.

Baya ga kasancewa daya daga cikin nau'ukan kayan kamshi da ake amfani da su wajen kara armashin girki, citta tana da dadadden tarihi na amfani a fannonin magungunan gargajiya da dama.

Masana harkokin abinci sun ce kamshi da dandano na musamman da citta ke da su na fitowa ne daga man da ake samu daga jikinta, kana mafi muhimmanci shi ne sinadarin 'gingerol' mai kunshe da sinadaran magani masu karfi.

Binciken masana

Masana kimiyya da suka gudanar da bincike mai zurfi a kan citta, da kuma kwararru a fannin hada magungunan gargajiya da sarrafa kayan kamshi, da saiwoyi da tsirrai, sun bayyana dimbin amfanin da citta ke da shi ga lafiyar jikin dan adam ta hanyoyi da dama.

Mujallar kiwon lafiya ta ''Healthline'' da ke Birtaniya ta wallafa binciken masana da ya gano wasu abubuwa game da citta da suka hada da magance ciwon gabobi, da rage kaifin kwayoyin halittar da ke haddasa cutar kansa a jikin dan adam da sauransu.

Masana daga Cibiyar Bincike ta Hormel a Jami'ar Jami'ar Minnesota ta Amurka sun gudanar da wani bincike mai zurfi game da citta a kan wasu beraye a shekarun baya, inda sakamakonsa ya nuna cewa sinadaran da ke jikin citta suna saurin kashe kwayoyin halittar cutar kansa.

Kazalika wani bincike na biyu da Kungiyar Masu Bincike kan Cutar Kansa ta Amurka ta gudanar ya nuna cewa cittar na rage kaifin yaduwar kwayoyin halittar kansar mafitsara.

Kuma akan yi amfani da ita wajen magance tashin zuciya, mura da kakamantansu kamar yadda binciken masana kimiyya ya nuna.

Nicola Shubrook, wata kwararriya a fannin abinci mai gina jiki da kula da lafiyar al'umma da ke Birtaniya wacce ta gudanar da bincike kan amfanin shayin citta, ta yi wa BBC karin bayani cewa citta tana da matukar amfani a jikin dan adam fiye da yadda ake tsammani.

Ta ce: "Citta tana taimakawa sosai wajen saukaka cutar hawan jini da kuma magance tashin zuciya da amai, musamman ida aka yi shayi da iya."

Malam Hambali Musa, wani dattijo ne mai shekaru 78 a Najeriya da yake yawan amfani da citta, ya shaida wa BBC cewa al'ummomi daban-daban a fadin duniya sun dade suna amfani da citta don maganin ciwon gabobi, ciwon jiki kuma har yanzu hakan bai sauya ba.

"Don saboda citta aba ce da muka dade da yin imanin cewa tana da wasu sinadarai da ke hana ciwon jiki bayan gudanar da aikin karfi, da sauran cututtuka kamar su mura," in ji Hambali.

A tattaunawarsa da BBC, Malama Bilkisu Lawal Zarabid, wata kwararriya a fannin sarrafa kayan kamshi, da itatuwa da ganyaye da sauran tsirrai, ta bayyana cewa citta na matukar taimakawa a fannoni da dama na lafiyar dan adam don haka yake da matukar muhimanci a rika amfani da ita.

Ta kuma ce ana sarrafa citta a danyarta, ko busasshiya ko garin ta, har ma da man ta, kuma mata masu fama da amai da tashin zuciya lokacin da suke laulayin ciki kan yi amfani da citta don dakatar da amai.

"Har ila yau mata masu fama da ciwon mara kan yi amfani da citta wajen magani, kana ana sarrafa ta da wasu saiwoyi wajen hada maganin ciwon suga, da mura da ciwon kasusuwa wato ''Athritis'', ana kuma amfani da ita wajen sarrafa maganin haihuwa a gargajiyance," in ji Zarabid.

Ita ma Dr Katherine Marengo, wata kwararriya a fannin kiwon lafiya da abinci mai gina jiki, ta bayyana wa mujallar Healthline cewa wani bincike da aka gudanar kan mata masu juna biyu 120 ya nuna cewa wadanda suka sha giram 750 na garin citta a kullum cikin kwanaki 4 sun shaida samun saukin tashin zuciya da amai, ba kamar matan da ba su sha ba.

Maganin gyambon ciki

Sai dai malama Bilkisu Lawal ta ce shan citta ga masu gyambon ciki da aka fi sani da 'ulcer' kan haifar musu da matsala sosai saboda zafin da take da shi, don haka ko ga wadanda ba su da irin wannan matsala bai kamata su rika amfani da ita fiye da kima ba.

"A ka'ida shan citta in dai sau daya za ka sha, bai wuce ka sha kamar yatsa daya ba, idan kuma za ka sarrafa ne zuwa abin sha da ake kira "ginger shot" bai wuce ka markada kamar yatsa biyar ba a yi lemon tsami saboda yana wanke ciki," in ji ta.

A cewarta: "Tana cikin sinadarai ta farko wajen kokarin rage kiba, saboda yana wanke ciki da sauran dattin ciki idan ka juri sha da lemon tsami zai taimaka matuka wajen rage kitse na jiki da tumbi.''

Ga jerin abubuwan amfanin da citta ke yi ga jikin dan adam

An samo bayanai game da amfanin citta a jikin dan adam daga kwararru a fannin sarrafa itatuwa ta tsairrai na gargajiya da kuma mujallun kiwon lafiya da suka wallafa binciken masana kimiyya a kai kamar haka:

  • Citta na taimakawa wajen bunkasa garkuwar jiki


  • Tana kare jikin mutum daga sanyi da wasu cututtuka


  • Tana taimakawa wajen dauke zafin cuta ko ciwo a jiki


  • Tana taimakawa wajen gudanar da yawan suga a jikin mutum


  • Citta na maganin ciwon gabobin jiki


  • Tana kuma magance rudewar ciki


  • Tana maganin ciwon mara na mata a lokacin jinin a'l'ada


  • Citta na saurin narkar da abinci


  • Tana taimaka wa wajen magance makaki ko kaikayin makogwaro


  • Citta na taimakwa wajen rage maikon jini maras kyau ''cholesterol''


  • Tana magance tashin zuciya da amai


  • Tana rage kaifin hadarin kamuwa da ciwon kansa


  • Tana maganin sany da mura


  • Citta na taimakawa wajen kawar da zafin kirji.


  • Citta na taimakawa wajen rage kiba da kuma narkar da abinci


  • Bincike ya nuna cewa citta na taimakwa wajen kare cutar mantuwa ko 'Alzheimer'


  • Citta na habaka gudanar jini a jiki kuma yana kara karfin jiki
  • Abin sha na citta

    Ana amfani da citta wajen sarrafa abin sha don na lemo ko shayi da akan hada da wasu sinadari don kara armashi.

    Ana amfani da danyar citta mai yawa wajen sarrafa abin sha na citta, da aka bayyana cewa yana taimakawa wajen bunkasa garkuwar jikin dan adama da kuma kare cutattauka kamar yadda Dr Katherine Marengo ta bayyana wa mujallar Healthline ta Birtaniya.

    "Duk da cewa abin sha na citta bai dade da zama sanannen abu ba a fannin kiwon lafiyar al'umma, amma tun a zamanin da ake amfani da ruwan maganin citta wajen warkar da cutattuka da dama," in ji Katherine.

    Ta kara da cewa: "Yayin da citta ke samar da sinadaran amfani ga jikin dan adam, za ka iya mamakin shin ko abin sha na cittar da aka sarrafa da gaske yana daamfani."

    Kayyakin da ake amfani da su wajen hada abin sha na citta sun danganta ga yadda ake son dandanonta ya kasance.

    Wasu sun kunshi ruwan danyar citta mai yawa da aka markada aka tace, yayin da wasu akan hada da ruwan lemon tsami, da kurkum da barkono da kuma zuma.

    "Za ka iya hada su wuri guda a cikin abin markade ka markada su sannan ka tace kafin ka sha," a cewarta.

    Ana kuma hadawa ne ta hanyar kankarewa ko markada danyar cittar a hada da lemon tsami ko na zaki a tace a rika sha.

    Akan kuma samu irin wannan abin sha a wasu manyan shagunan sayar da abinci mai gina jiki da kiwon lafiya.

    Saboda kauri da kuma karfin da citta ke da shi, abin sha din kan kasance mai yaji da kuma dandano mai kama baki wurin sha.

    Shayin citta

    Shayin citta ya samo asali ne daga kasar China a shekaru 5,000 da suka wuce kamar yadda mujallar kiwon lafiya ta Healthline ta wallafa, inda a gargajiyance ake amfani da shi a matsayin magani da kuma nishadi.

    Daga bisani ne shayin na citta ya bazu zuwa kasashen Turai inda har yanzu ake ci gaba da amfani da shi wanda a ka samu a manyan shaguna.

    Ana amfani da danyar citta mai yawa wajen sarrafa abin shayin citta, da aka bayyana cewa yana taimakawa wajen bunkasa garkuwar jikin dan adama da kuma kare cututtuka kamar yadda Nicola Shubrook, wacce ta gudanar da bincike kan amfanin shan shayin citta ga jikin dan adam ta bayyana wa BBC.

    Nicola ta ce ana sarrafa shayin na citta ta hanyoyi da dama, wanda ya danganta ga yadda kake son ka ji dandanon.

    Ta ce: "Ana amfani da busasshiya ko danyar citta wajen dafa shayin, ko kuma a jika shi a cikin tafasasshen ruwa na zuwa 'yan mintina, don man da ke jikin cittar ya tsattsafo kafin ka sha."

    Shayin citta na da gamsarwa, kuma yana da yaji a baki, amma in ji Nicola za ka iya kankarewa ko daddatsa cittar ka zuba a cikin kofi, ko ka sayi garin ta ko a yanayin cikin jakar ganyen shayi ka tsoma.

    Ana iya hada citta da wasu nau'ukan kayan kamshi wajen dafa shayin don kara armashi da kuma dandano.