Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 05 11Article 450705

BBC Hausa of Tuesday, 11 May 2021

Source: BBC

Cavani zai ci gaba da wasa a Man United kaka daya

Edison Cavani Edison Cavani

Edison Cavani ya cimma yarjejeniyar ci gaba da taka leada a Manchester United zuwa kaka daya, inda ake sa ran kungiyar za ta sanar da hakan nan gaba.

Cavani mai shekara 34 bai fayyace makomarsa a baya ba, sakamakon cin karo da wasu matsaloli a farkon zuwansa Old Trafford.

Kawo yanzu an kawo karshen matsalolin an kuma sanar da BBC cewar an cimma yarjejeniya ta ci gaba da zaama a Old Trafford tsakanin United da Cavani.

Kawo yanzu United ba ta tabbatar da hakan ba, amma nan da lokaci kadan kungiyar za ta sanar da batum.

Cavani na taka rawar gani a bana a United, inda ya ci kwallo bakawi a wasa takwas, jumulla 15 ya zura a raga har da wadda ya ci Aston Villa ranar Lahadi a gasar Premier League.

Manchester United tana mataki na biyu a teburin Premier League da tazarar maki 10 tsakaninta da Manchester City ta daya.

United din za ta buga wasan karshe a Europa League da Villareal, karon farko da Ole Gunnar Solskjaer ya kai kungiyar wasan karshe tun bayan da ya zama koci.