Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 05 28Article 451014

BBC Hausa of Friday, 28 May 2021

Source: BBC

Bincike ya gano cewa bakaken fata 'sun fi fararen fata jin zafi' a Amurka

Bakake da ke zaune biranen Amurka sun nunka fararen fata wajen jin zafi, inji wani bincike Bakake da ke zaune biranen Amurka sun nunka fararen fata wajen jin zafi, inji wani bincike

Wani sabon bincike ya gano cewa bakaken fatar da ke zaune a galibin biranen Amurka sun nunka fararen fata wajen jin zafi.

Mutanen da suka gudanar da binciken sun ce ba talauci ne ya jawo wannan bambanci na jin zafi ba sai dai domin tarihin wariyar launin fata da kebewar da ake yi wa bakaken fata.

Sakamakon hakan, yawancin mutanen da ba turawa suna zaune a yankunan da babu bishiyoyi sosai sannan akwai gidaje a cunkushe da hanyoyi.

Hakan ya ta'azzara karuwar dumamar yanayi da sauyin yanayin.

Birane sun yi suna wajen taimakawa kara yanayi mai dumi.

Binciken ya nuna yadda gine-gine da hanyoyi da ababen more rayuwa suke yin tasiri a kan yanayi.

Gidajen da ake yi da kankare da kuma hanyoyin kwalta suna kara yanayin zafi, abin da ya sa dare da rana suke cikin yanayi na dumi idan aka kwatanta da yankunan karkara.

Sai dai a cikin birane, akwai bambancin yanayin zafi tsakanin yankunan da ake da bishiyoyi inda suke da yanayi mai dadin zama, da kuma wuraren da gidaje suke a cunkushe da kuma masana'antu.

Wani rahoto da aka gudanar a baya ya gano dangantakar da ke tsakanin yankunan da ke da yanayi mai dumi a manyan birane da kuma wariyar launin fata da ake nunawa wajen bayar da damar gina gidaje tun daga shekarun 1930.

A wadancan shekarun, yankunan da Amurkawa 'yan asalin Afirka ko kuma 'yan ci-rani suka fi zama, an yi musu tambari da cewa suna da "matsala" a cewar wasu bayanai na jami'an gwamnatin tarayya, don haka aka ayyana su a matsayin masu hatsari wajen karbar bashin gidaje ko zuba jari.

Hakan ya sa talauci ya yi katutu sannan ba a samun mutanen da suka mallaki gidaje a wasu manyan biranen Amurka.

Wannan sabon binciken ya yi duba na tsanaki kan yankunan da ke da dumi da kuma mutanen da hakan ya shafa.

Ta hanyar amfani da bayanan da aka tattaro daga tauraron dan adam kan yanayi hadi da alkaluman kidaya na Amurka, masu bincike sun gano cewa galibin mutanen da ba turawa ba suna zaune a yankunan da ke da zafi sosai a lokacin bazara idan aka kwatanta da turawa.

A binciken, masana kimiyya sun bayyana cewa "mutanen da ba turawa ba" sun hada da dukkan 'yan asalin kasashen da ke magana da yaren Sifaniya da kuma duk wanda ba bature ba ne.

A dukkan yankunan manyan birane 175 na Amurka idan ban da shida, mutanen da ba turawa ba suna fama da tasirin matsanancin zafi a lokacin bazara.

Hakan ya fi tasiri karara kan bakaken fata. Masu binciken sun ce suna fama da karin zafi na ma'aunin zafi 3.12C a yankunan birane, idan aka kwatanta da turawa da ke fama da karin zafi na 1.47C.

Tsananin zafi yana iya kai wa ga mutuwa, kuma tasirinsa ya hada da yin aiki kasa da yadda ya kamata da kuma nakasu wajen koyon karatu a makaranta.

"Bincikenmu ya taimaka wajen samar da kwararan shaidu game da nuna wariyar launin fata kan yanayi da kuma muhalli," a cewar Dr Angel Hsu, daga Jami'ar North Carolina-Chapel Hill, malamar da ta jagoranci masu binciken.

"Wannan lamari ya shafi dukkan Amurka don haka ba wai abu ne da yake a wasu kebabbun wurare ba."

An wallafa binciken a mujallar Nature Communications.