Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 03 12Article 449618

BBC Hausa of Friday, 12 March 2021

Source: BBC

Babagana Monguno: Bamu gano inda kudin makamai suke ba

Mai bai wa shugaban Najeriya shawawar kan harkokin tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno Mai bai wa shugaban Najeriya shawawar kan harkokin tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno

Mai bai wa shugaban Najeriya shawawar kan harkokin tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno ya ce har yanzu ba a san yadda aka yi da makudan kudaden da shugaba Buhari ya bayar don sayen makamai da sauran kayan aiki don yaki da matsallolin tsaro da suka addabi kasar ba.

A hirarsa da BBC Monguno ya bayyana cewa gwamnati na bakin kokarinta wajen shawo kan matsalar tsaron da ake ci gaba da fuskanta, da wasu 'yan Najeiya ke ganin gwamnati ba da gaske ta ke yi ba domin tana ta jan kafa game da al'amarin.

    Rashin tsaro: Abin da ya sa gwamnatin Najeriya ta kasa maganin masu satar mutane GGSS Jangebe: Me ya sa ake satar ɗalibai a Najeriya?
''Babu wanda ya san me aka yi da wadannan kudaden, amma kuma da yardar Allah shugaban kasa zai bincika domin a gano inda aka kai kudaden ko kuma a ina kayan suka shiga,'' in ji Monguno .

Kungiyar gwamnoni ma in ji jami'in tsaron sun fara magana a kan cewa "an bayar da kudade ta ko ina amma babu abin da aka yi da su, saboda haka na tabbatar shugaban kasa tun da ba mai wasa da hakkin al'umma bane, zai taimaka."

Munguno ya jaddada cewa: "Tun da dai ba a yi wani binciken kwarai ba, ba zan ce wani abu ba, amma dai kudi dai tabbas sun salwanta, kayan dai ba a gani ba, kuma sabbin shugabannin tsaro sun ce su fa ba su ga kayyakin tsaro da ake magana ba a kai.

"Ƙila wasu suna kan hanya daga Amurka, daga Ingila ko daga wasu wurare, amma yanzu a kasa ban gani ba su ma ba su gai ba," in ji shi.

Kan batun gwamnati na sakaci da al'amuran tsaro a kasar sai yace ''Ba jan kafa ba ne ya janyo wannan matsalar shugaban kasa ya yi iya bakin kokarinsa ya bayar da kudade na fitar hankali amma ba a sayo kayan ba, saboda haka yanzu ya kawo sabbin mutane mai yiwuwa za su samu wata dabara da za su yi."

Duk da cewa bai fito kai tsaye ya ce manyan hafsoshin sojan da aka sauke sun cinye kudin sayen makaman ba, amma ya yi jirwaye mai kamar wanka.

Ya ce shi ba zai iya cewa ko wadanda suka yi murabus din sun yi sama da fadi da kudin ba, amma dai abinda zai ce shi ne babu wanda ya san abinda aka yi da kudin tun da har yanzu ba a ga kaya a kasa ba.

A watan janairu ne Shugaban Najeriya ya sauke hafsoshin tsaron ƙasar kuma ya sanar da sabbi.

Hafsoshin sojin sun ƙunshi babban hafsan tsaron ƙasar Janar Abayomi Olonisakin; da babban hafsan sojin ƙasa Janar Tukur Buratai; da babban hafsan sojin sojan ruwa Vice Admiral Ibok Ekwe Ibas; da babban hafsan sojin sama Air Marshal Sadique Abubakar.

Shugaban ya naɗa Janar Leo Irabor a matsayin babban hafsan tsaro da Janar Ibrahim Attahiru a matsayin babban hafsan sojan ƙasa da Rear Admiral Gambo - babban hafsan sojan ruwa sai Air-Vice Marshal Amao a matsayin babban hafsan sojan sama.