Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 03 04Article 449482

BBC Hausa of Thursday, 4 March 2021

Source: BBC

Ba ma goyon bayan muƙabala da Abduljabbar - JNI

Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III

Kungiyar Jama'atu Nasril Islam karkashin shugabancin mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III ta ce ba ta ga dalilin da zai sa a yi muƙabala da Abduljabbar Nasiru Kabara ba da sauran malamai ba.

Cikin wata sanarwa da sakataren ƙungiyar Dakta Khalid Abubakar Aliyu ya fitar ta ce tun daga farkon turka-turkar, gwamnatin Kano ta yi abin da ya dace wajen ganin abubuwan da suke faruwa ba su fi ƙarfinta ba.

Sai dai ta ce da gwamnatin ta tuntuɓi mutane da dama kamar yadda ya kamata wajen shawo kan lamarin da ba a ba ta shawarar haɗa wannan muƙabala ba, saboda ba abu ba ne da ya shafi jihar Kano kadai ba, matsala ce da ta shafi duk wani Musulmin Najeriya da duniya baki ɗaya.

"Don haka haɗa wannan muƙabala na nufin mayar da Abduljabbar wani gwarzo a cikin al'umma, kuma bai cancanci hakan ba a matsayinsa na mai jan ƙasƙanci ga fiyayyen halittta da iyalan gidansa da sahabbansa," in ji sanarwar.

Sai dai gwamnatin jihar Kanon ta ce hukunci yana hannun malaman jihar da dama su suka nemi a yi mukabalar, a cewar kwamishinan yada labarai Muhammad Garba.

Amma ita ma Majalisar Malaman jihar ta ce ba ta ɗauki matsaya dangane da buƙatar ƙungiyar Jama'atu Nasril Islam ba a yanzu.

Sai dai tuni sun miƙa sunayen malaman da za su yi muƙabalar da Sheikh Abduljabbar amma ba za su bayyan sunayensu ba sai a ranar.

Sanarwar ta kara da cewa duba da tanade-tanaden fiƙihu, JNI na ganin cewa bai kamata a yi wannan tattaunawa da Abduljabbar ba, wanda yake yin ɓatanci a bayyane ga Annabi Muhammad ba.

"Imaninsa ya raunana a koyarwar addini Musulunci, babu wani dalilin da zai sa a ƙara ba shi damar da zai ci gaba da yaɗa manufarsa ta rashin tsoron Allah ga duniya.

"Da gwamnatin Kano ta tuntuɓi mutanen da ya kamata kan maganar muƙabalar da an kaucewa duk matsalolin da aka bayyana a sama.

"Don haka JNI ba za ta halarci wannan mukabalar kuma babu wani daga cikin mambobinta ko reshenta da zai halarci wajen taron.

"Muna yi wa gwamnatin Kano da Malamai fatan alkhairi a duka shirye-shiryensu. Haka kuma muna yi wa masu ruwa da tsaki da gwamnati fatan su sake duba matsayarsu kan wannan batu," kamar yadda sanarwar ta ƙara da cewa.

An shirya gudanar da muƙabala tsakanin Sheikh Abduljabbar da wasu manyan malaman Kano a ranar Lahadi mai zuwa, sakamakon zargi malamin da gwamnatin Kano ta yi na "kalaman tayar da fitina game da addinin Musulunci" bayan wasu malamai a jihar sun zarge shi da saɓa wa abin da Musulunci ya zo da shi.