Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 05 29Article 451041

BBC Hausa of Saturday, 29 May 2021

Source: BBC

BBC Hausa: Ƙa'idojin shiga Gasar Hikayata 2021

Hikayata wata Gasar Rubutun Ƙagaggun Labarai ta Mata ta BBC Hausa Hikayata wata Gasar Rubutun Ƙagaggun Labarai ta Mata ta BBC Hausa

Latsa nan don karanta Sanarwa Game da Tsare Sirrin Masu Shiga Gasar Hikayata ta BBC Hausa

Gasar Rubutun Ƙagaggun Labarai ta Mata ta BBC Hausa, Hikayata.

Ƙa'idojin Shiga Gasar:

1.Dole ne duk wani labari da za a turo da nufin shiga gasar Hikyata ya cika waɗannan sharuɗɗan:

1.1.Dole ne labarin ya kasance gajere da bai haura kalma 1,000 zuwa 1,500;

1.2.Wajibi labarin ya kasance mace ce ko mata ne suka rubuta shi;

1.3.Lallai ne labarin ya kasance cikin ingantacciyar Hausa, da bin duka ƙa'idojin rubutu;

1.4.Wajibi ne mai turo da labarin ta kasance ta kai shekara 18 da haihuwa ko sama da haka. Ga masu turo da labarin haɗin guiwa, wajibi ne ko waccensu ta kasance shekararta 18 ko sama da haka;

1.5.Dole ne wadda za ta turo da labarin ta zama ita ce ainihin wadda ta rubuta shi; ba a yarda wata ta aiko da labarin da wata ko wani suka rubuta ba;

1.6.Mata biyu za su iya shigar da labari ɗaya a gasar, amma kada su wuce haka;

1.7.Ba a yarda mace ɗaya ta aiko da labari fiye da ɗaya ba;

1.8.Bai kamata rubutun ya ƙunshi wasu kalmomi da suka shafi batsa ba, ko yaba wa ta'addanci, ko ɓata wa yara ko kuma wasu gungun al'umma suna ba;

1.9.Matakin da alƙalai za su dauka a kan cancantar labarin da aka turo shi ne na ƙarshe. Ba za a iya ƙalubalantar hukuncin ba. BBC za ta watsa wasu daga cikin labaran da aka zaɓa a shirye-shiryenta, kuma za ta yi hakan ne da izinin masu rubutun.

Za kuma a iya wallafa wasu daga cikin labaran a wani littafi, wanda kawo yanzu ba a tabbatar da yadda zai kasance ba, kuma hakan zai dogara ne da amincewar BBC. Ba tilas ba ne BBC ta watsa ko ta wallafa kowanne daga cikin labaran da aka turo.

2.Turo da Labari:

2.1.Za a aiko da labaran ne ta email zuwa ga: labari.bbchausa@bbc.co.uk tare da waɗannan bayanai na mai aikowar:

  • Suna (ko sunaye ga masu aiko da labarin haɗin-guiwa)


  • Lambar waya (ko lambobin wayar ko wacce daga cikin masu aiko da labarin haɗin guiwa)


  • Adireshi (ga masu turo labarin haɗin guiwa, adireshin ko wacce)


  • Adireshin email (ga masu turo labarin haɗin guiwa, adireshin email na ko wacce)


  • Taƙaitaccen bayani game da labarin


  • Gajeren tarihi (ga masu turo labarin haɗin guiwa, gajeren tarihin ko wacce). Misali- Me ya sa kika fara rubutu? Yaushe kika fara rubutu? Waɗanne irin labarai kika fi son karantawa?


  • 2.2. Ba za a karɓi duk wani labari da bai cika waɗannan sharuɗɗa ba.

    2.3. Ba a yarda ma'aikatan BBC ko 'yan uwansu su shiga wannan gasa ba.

    2.4. BBC za ta yi aiki da duk wani bayani da mai shiga gasar ta aiko game da kanta, ta hanyar bin dokokin kare bayanai da aiki da Sanarwa Game da Tsare Sirrin Masu Shiga Gasar Hikayata ta BBC Hausa (za ku samu wannan a ƙasan wannan shafin)

    2.5. Ba a yarda marubutan da suka yi zarra a gasar baya su shiga ta bana ba.

    3. An buɗe shiga gasar da ƙarfe 10.00 agogon GMT, wato karfe 11.00 agogon Najeriya da Nijar ranar 31 ga watan Mayun 2021.

    4. Za a rufe karɓar labarai ranar 16 ga watan Agusta 2021 da ƙarfe 11.59 agogon GMT. Duk wacce ta aiko da labarinta bayan nan ba za a karɓa ba.

    Za ki ga saƙon godiya bayan kin aiko da labarinki. Sai dai kuma saboda yawan saƙonnin da muke samu, ba zai yiwu mu amsa tambaya game da ko wanne labari ba.

    5. Wajibi ne labarin da za a aiko ya kasance aikin wadda ta turo da shi, kuma ya dace da ƙa'idojin da aka shimfiɗa. Kada labarin ya shiga haƙƙin wani (wanda ya haɗa da bayanan sirri), kuma kada a ɓata wa wani suna ko a aikata abin da ya saɓa wa doka.

    BBC ba za ta ɗauki alhakin komai ba idan masu shiga wannan gasa suka yi biris da waɗannan ƙa'idoji, sannan kuma masu shiga gasar sun amince su bai wa BBC cikakkiyar kariya daga duk wani iƙirari da wani zai yi sakamakon yin karan-tsaye ga waɗannan ka'idoji.

    6. Idan aka zaɓi labari ya kai mataki na gaba, to za a nemi wadda ta turo da shi ta cike wani fom wanda zai bai wa BBC damar watsa labarin, za kuma a iya buƙatar marubuciyar ta naɗi labarinta domin a watsa.

    Idan BBC ta yanke shawarar wallafa littafi mai ɗauke da wasu daga cikin labaran da aka zaɓa, fom din zai ba ta damar sanya labarin a cikin littafin.

    Waɗanda suka yi ta ɗaya, da ta biyu, da ta uku ne kawai za su samu kyauta: Dalar Amurka 2,000 da lambar yabo ga labarin da ya zo na ɗaya; dalar Amurka 1,000 da lambar yabo ga labarin da ya zo na biyu; da dalar Amurka 500 da lambar yabo ga labarin da ya yi na uku. Za kuma a ambaci marubuta waɗansu labaran waɗanda suka cancanci yabo.

    7. Duk wacce ta turo da labarinta, to ta amince kenan ta yi aiki da sharuddan da wadannan ka'idoji suka gindaya.

    8. Matakin Farko - Tantancewa

    A cikin ma'aunin da za a yi amfani da shi don tantance labaran da aka turo akwai:

  • Labari ya kasance ƙirƙirar shi aka yi, ma'ana ba kwafo shi aka yi ba.


  • Amfani da ƙwarewa, ma'ana labari ya zama mai jan hankali da taurarin da suka dace;


  • Bin ƙa'idojin nahawu da na rubutun Hausa


  • 9. Wasu kwararru za su tantance dukkan labaran bisa ƙa'idojin da aka shimfida, sannan su zaɓi labarai 25.

    Daga nan za a miƙa labaran da aka zaɓa ko aka tantance ga alƙalan gasar. Za a sanar da waɗanda aka zaɓi labaransu yayin wannan tantancewa a makon da ke farawa daga ranar 23 ga watan Satumba 2021.

    10. Mataki na Biyu - Matakin Alƙalanci da zaben labarin da ya yi zarra

    10.1. Alƙalan za su karanta su kuma tattauna kan labaran.

    10.2. Za a sanar da marubuta ukun da labaransu suka yi zarra tsakanin ranakun 28 zuwa 29 ga watan Octoba 2021.

    11. Hukuncin alƙalan shi ne na ƙarshe. Ba za a tuntuɓi waɗanda ba su yi nasara ba kuma ba za a mayar musu da amsa kan labaran da suka turo ba.

    12. BBC ka iya gayyatar waɗanda suka yi nasara da wasu waɗanda labaransu suka cancanci yabo, domin halartar taron bayar da kyaututtuka a Abuja. (BBC za ta ɗauki nauyin kuɗin mota da masauki wanda bai wuce ƙima ba.

    Waɗanda aka gayyata su ne ke da alhakin nema wa kansu izinin shiga Najeriya idan su ba 'yan kasar ba ne).

    13. BBC na da ikon soke ko cire dukkan labarin da ya saɓa wa ko wanne daga cikin waɗannan ƙa'idojin.

    14. BBC na da ikon sauya waɗannan ƙa'idojin a kowanne lokaci, ciki har da sauya hanyoyin zaɓen ko kuma alƙalan. Idan hakan ta kasance, to za a sanar a wannan shafin na intanet: bbchausa.com.

    15. An tsara waɗannan Ƙa'idojin ne bisa tanade-tanaden dokokin Ingila da Wales.

    Sanarwa Game da Tsare Sirrin Masu Shiga Gasar Hikayata ta BBC Hausa

    Yardarki na da muhimmanci a garemu. Wannan na nufin cewa BBC ta ɗaura ɗamarar kare bayananki. Yana da muhimmanci ki karanta wannan sanarwar don sanin yadda muke amfani da bayananki da kuma dalilin da ya sa muke amfani da su.

    Wannan sanarwa ta ƙunshi yadda muke karɓa da amfani da bayanai game da ke a yayin da kuma bayan mu'amalarki da mu, kamar yadda dokar tsare sirri ta tanada. Za ki iya samun ƙarin bayani a nan. Kina iya samun ƙarin bayani kan bayani da tsare sirri.

    Me muke karɓa kuma ta yaya za mu yi amfani da shi?

    Idan shekarunki sun kai 18 ko sun haura, muna maraba da shigarki gasar. Don shiga gasar, BBC za ta karɓa kuma ta yi aiki da bayanan da suka shafe ki waɗanda kika aiko mana, ciki har da sunanki da lambar wayarki da adireshinki na gida da adireshinki na email da duk wani bayani game da ke da kika aiko mana dangane da shigarki gasar.

    Za a yi amfani da bayanan da kika aiko mana da manufar shiga gasar. BBC ce 'mai iko' kan wannan bayani. Hakan na nufin cewa BBC ce za ta yanke shawarar abin da za a yi da bayananki, da hanyoyin da za a yi amfani da su.

    Idan buƙatunki ba su kere na BBC ba, BBC za ta yi aiki da bayananki dangane da wannan gasa bisa buƙatunta (wato BBC) da ba su kauce wa ƙa'ida ba na - nishaɗantar da masu bibiyarta da shirya gasanni bisa gaskiya da sanin ya kamata.

    Ajiye bayananki

    Idan ke ce kika yi nasara a gasar, ko kuma kika zo ta biyu ko ta uku, ko kuma kina ɗaya daga cikin mutane goma sha biyu da labaransu suka cancanci yabo za a wallafa labarinki sannan BBC za ta ajiye bayananki tsawon shekaru biyu.

    Za a goge labaran da ba su yi nasara ba, bayan an sanar da waɗanda suka yi nasara ranar 26 ga watan Nuwamba, 2021.

    BBC za ta aika labarinki ga alƙalan gasar waɗanda ba ma'aikatan BBC ba ne.

    Ma'aikatan BBC da ke London da Najeriya za su ajiye bayananki a kamfutocin BBC tare da ɗaukar matakan tsaron da suka dace.

    Muna iya nemanki don tabbatar da shekarunki ko don mu tattauna kan labarin da kika shigar gasar.

    Haƙƙinki da Ƙarin bayani

    Idan kina da wata tambaya kan yadda BBc ke tafi da bayananki, ko kuma kina so ki san haƙƙoƙinki, ki ziyarci wannan shafin na BBC. Za kuma ki samu ƙarin bayani kan yadda BBC ke aiki da bayananki da yadda za ki iya aika saƙo ga Jami'in da ke Kula da Kare Bayanai na BBC.

    Idan kika nuna wata damuwa dangane da yadda BBC ke aiki da bayananki kuma ba ki gamsu da amsar da BBC ta ba ki ba, kina da ikon shigar da ƙorafi ga wata hukuma mai sa ido. A Burtaniya, hukumar da ke sa ido ita ce Ofishin Kwamishinan Bayanai (ICO).