Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 05 28Article 451011

BBC Hausa of Friday, 28 May 2021

Source: BBC

Antonio Conte ya bar Inter Milan bayan lashe Serie A

Antonio Conte, tsohon kocin Inter Milan Antonio Conte, tsohon kocin Inter Milan

Antonio Conte ya bar aikin horar da Inter Milan - wata daya tsakani bayan lashe Serie A a karon farko da kungiyar ta yi wannan bajintar tun bayan shekara 11.

Mai shekara 51 dan kasar Italiya ya yi kaka biyu a Inter, kuma saura kwantiragin shekara daya ya kare a kungiyar.

A wani jawabi da Inter ta fitar ta yi godiya ga Conte kan namijin kokarin da ya yi wa kungiyar a aikin da ya gudanar.

Tun a baya ana alakanta Conte da cewar zai koma Real Madrid da horar da tamaula, bayan da ake cewar Zinedine Zidane zai bar aiki a karshen kakar bana.

Haka kuma ana alakanta Conte da cewar zai koma kocin Tottenham, bayan da ya taba taka rawar gani a Chelsea da aka yaba masa.

Sai dai duk da cewar ya taimakawa Inter ta lashe gasar Italiya da kuma Juventus, wasu na yin hasashen makomar tsohon kocin Chelsea a dan watannin nan.

An ruwaito cewar mai kungiyar Inter, Suning daga China na fuskantar kalubalen kudi, wanda hakan ne ya sa ya bi wannan matakin don rage kashe kudi da yawa, zai kuma sayar da 'yan wasa da yawa.

Ana alakanta tsohon kocin Juventus, Massimiliano Allegri da wanda ke jan ragamar Lazio, Simone Inzaghi cikin wadanda ake sa ran za su maye gurbin Conte.