Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 06 03Article 451130

BBC Hausa of Thursday, 3 June 2021

Source: BBC

Antonio Conte: Tottenham ta tuntubi tsohon kocin Chelsea

Antonio Conte, tsohon kocin Inter Milan Antonio Conte, tsohon kocin Inter Milan

Tottenham ta tuntubi tsohon kocin Chelsea, Antonio Conte don nada shi sabon mai horar da tamaula a kungiyar.

Babu wani tayi da aka yi kawo yanzu, amma an fahimci Tottenham ta tattauna da kocin dan kasar Italiya.

Conte ya lashe Serie A da Inter Milan a bana, kofin farko da kungiyar ta dauka tun bayan 2010 a watan jiya, daga baya ya bar kungiyar, bayan cimma yarjejeniya da mai Inter, Steven Zhang.

Tottenham ta yi wa tsohon kocinta Mauricio Pochottino tayin ko zai sake karbar aikin jan ragamar kungiyar a makon jiya.

Sai dai kuma Paris St Germain ba ta da shirin rabuwa da dan kasar Argentinan.

Tottenham ba ta da koci tun bayan da ta kori Jose Mourinho ranar 19 ga watan Afirilu ta nada na rikon kwarya Ryan Mason.

Spurs ta kammala kakar Premier ta kakar nan a mataki na bakwai a teburi, ta kuma samu gurbin buga Europa League na badi.

Conte ya lashe kofin Premier League a 2016/17 a kakar farko da ya karbi akin kocin Chelsea, amma ta sallame shi bayan da ya ci FA Cup da yin na biyar a teburi a kaka ta biyu a Stamford Bridge.

Mai shekara 51 ya ja ragamar Inter zuwa gasar Europa League ta 2019/20 da kuma tazarar maki biyu tsakaninsa da Juventus wadda ta lashe kofin bara.

Amma a bana Inter ta dauki Serie A da tazarar maki 21 tsakaninta da Juventus ta hudu a teburin babbar gasar Italiya, ya kuma kawo karshen Serie A tara da Juventus ta lashe a jere.

Inter ta dauki Serie A na bana kuma na 19 jumulla tun saura wasa hur-hudu a karkare kakar bana da maki 91, ita ce ta biyu a tarihi da ta kammala wasannin da maki da yawa.