Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 05 27Article 450999

BBC Hausa of Thursday, 27 May 2021

Source: BBC

Ana fargabar fiye da mutum 100 sun mutu a hatsarin jirgin ruwa a Kebbi

Jirgin ya rabe gida biyu ya kuma nutse, inji labarai Jirgin ya rabe gida biyu ya kuma nutse, inji labarai

Gomman mutane ne ake fargabar sun mutu bayan wani jirgin ruwan da suke tafiya a cikin ya nutse a wani kogi da ke jihar Kebbi a arewacin Najeriya.

Lamarin ya faru ne yau Laraba da misali karfe 10 na safe, kuma bayanan da ke fitowa daga yankin na cewa kawo yanzu ana ƙoƙarin ceto waɗanda ya rutsa da su.

Bayanai dai na cewa jirgin ya taso ne daga Lokon Minna a jihar Neja zuwa garin Wara jihar na Kebbi dauke da mutane sama ga 160 da suka hada da maza da mata da ƙananan yara.

Amma sai ya rabe gida biyu ya kuma nutse tare da dukkan mutanen da ke cikinsa ana dab da isa garin na Wara.

Shaidu dai sun ce baya ga ɗauko ninkin adadin mutanen da ya kamata ya ɗauka, an kuma saka masa buhunan yashi da ake haƙowa daga mahaƙar zinare.

Shugaban karamar Hukumar Ngaski ta jihar Kebbi Abdullahi Buhari Warah wanda ya ziyarci wajen da lamarin ya faru don sa ido a aikin ceton ya ce lamarin akwai ban tausayi.

"A haƙiƙanin gaskiya mun je babban bakin kogin da ke garin Wara inda akwai mutanen da ke kuka idan suka fito daga cikin ruwan. Akwai mutum sama da 160 a cikin jirgin.

"Wani da ya fito daga cikin jirgin ya ce babu ceto kuma akwai ƙananan yara da dama da suka nutse a tekun don babu mai cetonsu.

"Akwai ma wani dan jihar Zamfara da ya ce min akwai wasu yan gida daya su takwas kuma duk sun niutse.

Wasu labaran da za ku so

Ya ce zuwa yanzu ba za a iya tantance adadin mutanen da suka rasa rayukansu ba, "akwai mutum 22 da aka ceto daga wasu bangarori na sassan wasu ƙauyuka da ke kusa kogin an kuma kai su asibitin Wara

"Sannan gawa ɗaya kawai aka samo zuwa yanzu ta wata yarinya.

Hon. Abdullahi Buhari ya ƙara da cewa a ƙa'ida jirgin yana ɗaukar mutum 65 ne zuwa 80 amma sai ga shi ya lodi mutum 160.

Sai dai Honorobul ya ce ba laifin hukumomin Kebbi ba ne ta wajen yin lodin da ya fi ƙarfin jirgin da kuma ƙin sa rigar da ke hana nutsewa.

"Yanzu haka muna bayar da jirage bakwai ga sarkin ruwa da wasu masu aikin ceto don lalubo gawarwaki da kuma wasu da ke da sauran rai.

Daga cikin fasinjojin jirgin dai akwai wadanda ke suka sa rigar kariya daga nutsewa amma kuma sai suka cire suka ba wasu saboda a cewarsu akwai zafi.

Hadari irin wannan dai ba bakon abu bane a wannan yankin na jihar Kebbi kuma yawanci akan danganta su ga daukar mutane fiye da kima da kuma yadda jiragen ke cin karon da kututtutan itatuwan ke tsirowa a cikin kogin.

Ko a wata Satumban bara hadarin irin wannan a jihar ta Kebbi ya yi sanadin mutuwar mutum takwas