Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 04 10Article 450146

BBC Hausa of Saturday, 10 April 2021

Source: BBC

An shiga rana ta biyu ta mutuwar Yarima Philip

Yarima Philip tare da Sarauniyar Ingila Yarima Philip tare da Sarauniyar Ingila

Gaba a yau Asabar ne ake sa ran Fadar Masarautar Ingila za ta fitar da bayanai game da jana'izar Duke na Edinburgh kuma za a yi harbin bindiga na girmamawa sau 41 a sassan Burtaniya.

Shirye-shiryen da aka yi tun da farko ya shafi baki 800 amma da alamu hakan zai sauya saboda ka'idojin da aka gindaya saboda cutar korona.

Ana sa ran gudanar da jana'izar a Fadar Windsor sai dai za a takaita adadin mutanen da za su halarta.

Cikin dare an rika ajiye furanni a wajen Fadar Buckingham da Windsor.

An bukaci mutane su guji taruwa saboda annobar korona.

An dai shiga rana ta biyu da Burtaniya da Masarautar Ingila ke jimamin mutuwar Duke na Edinburgh.

Yarima Philip wanda ya kasance tare da Sarauniyar Ingila fiye da shekara 70 ya mutu ne a Fadar Windsor jiya Juma'a.

Za a yi kasa-kasa da tutoci har zuwa lokacin jana'izar.

Babban dan Sarauniyar Ingila, Yarima Charles cikin wani shiri na musamman da aka nada kafin mutuwar Yarima Philip, ya ce irin gudummawar da mahaifinsa ke bai wa Sarauniyar Ingila abin jinjinawa ne.

Yarima Charles ke cewa ya kasance mai jajircewa wajen tallafawa mahaifiyata da yadda ya yi hakan na tsawon lokaci, kuma, ta wata hanya mai ban mamaki, yadda ya ci gaba da yin hakan tsawon lokaci ba tare da gajiyawa ba.

Yarsu daya tilo Gimbiya Anne ita ma tana da irin wannan ra'ayin.

Wata sanarwa da aka wallafa a shafin intanet na jikan marigayin wato Duke na Sussex Yarima Harry da matarsa Meghan da a yanzu haka suke zaune a Amurka ta bayyana yadda za a yi kewar Yarima Philip inda kuma ya yaba masa bisa irin jajircewarsa a lokacin da yake raye.

Ana kuma ci gaba da mika sakonnin ta'aziyya bisa mutuwar Duke na Edinburgh daga sassan duniya.

Firaministan Australiya, Scott Morrison ya ce Yarima Phillip mutum ne da ya sadaukar da rayuwarsa ga aiki inda ya ce Kungiyar kasashen Commonwealth suna tare da Masarautar Ingila a wannan lokaci.

Tun da farko tsofaffin shugabannin Amurka sun mika sakon ta'aziyyar mutuwar Yarima Philip kuma mijin sarauniyar Ingila.

Joe Biden ya yaba da yadda marigayin ya sadaukar da kansa wajen hidimtawa Sarauniyar Ingila . A Turai, shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana rayuwar marigayin a matsayin abin koyi