Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 06 07Article 451161

BBC Hausa of Monday, 7 June 2021

Source: BBC

An dage raba jadawalin gasar kofin nahiyar Afirka

An shirya bikin da aka dawka ne a Yaounden Kamaru ranar 25 ga watan Yuni An shirya bikin da aka dawka ne a Yaounden Kamaru ranar 25 ga watan Yuni

An dage bikin fitar da jadawalin gasar cin kofin nahiyar Afirka da aka tsara a Yaounden Kamaru ranar 25 ga watan Yuni.

Hukumar kwallon kafar Afirka, CAF ce ta sanar da hakan a ranar Lahadi.

Hukumar ta ce ta ci karo da cikas wajen tsare-tsare da suka shafi hana yada cutar korona, amma nan gaba za ta sanar da sabuwar ranar da za a yi bikin.

A cikin watan nan Saliyo da Benin suka buga kwantan wasa kuma na karshe don tantance kasashe 24 da za su fafata a gasar cin kofin nahiyar Afirka da Kamaru za ta karbi bakunci cikin watan Janairu.

Tun a bara ya kamata a buga gasar, amma cutar korona ta haddasa da aka kawo wasannin zuwa shekarar 2021.

A watan jiya CAF ta dakatar da wasannin neman shiga gasar cin kofin duniya da aka tsara fara yi a farkon watan Yuni, don gudun yada cutar korona.

Yanzu an tsayar da cikin watan Satumba, domin buga wasannin neman shiga gasar kofin duniya ta Qatar 2022 da shiyyar Afirka za ta barje gumu.