Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 04 06Article 450044

BBC Hausa of Tuesday, 6 April 2021

Source: BBC

Akalla mutum 50 sun mutu sanadin ambaliyar ruwa da zaftarewar kasa a Indonesia

Akalla mutum 50 ne suka rasa rayukansu sanadin ambaliyar ruwa a Indonesia da Timor Leste Akalla mutum 50 ne suka rasa rayukansu sanadin ambaliyar ruwa a Indonesia da Timor Leste

Akalla mutum 50 ne suka rasa rayukansu sanadin ambaliyar ruwa da zaftarewar kasa a Indonesia da Timor Leste a ranar Lahadi.

Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya yi barna sosai a wurare da dama tare da ambaliyar ruwa daga madatsun ruwa da suka fashe abin da ya shafi dubban gidaje da ke tsibiran biyu.

Yankin da iftila'in ya shafa ya faro ne daga tsibirin Flores da ke gabashin Indonesia zuwa makwabciyar kasar Timor Leste.

Ma'aikatan ceto na kokarin neman masu sauran numfashi kuma jami'ai sun yi gargadin cewa adadin wadanda suka hallaka zai karu.

Kakakin hukumar agajin gaggawa ta kasar, Raditya Jati ya fada wa maneman labarai cewa "kananan hukumomi hudu da kauyuka bakwai ne iftilain ya shafa."

Bayan da muka tabbatar da bayanan tare da tawagarmu da ke filin, mun gano cewa mutum 41 sun mutu kuma 27 sun bata yayin da tara sun jikkata.

Sai dai wani jami'i a East Flores ya yi kiyasin kimanin mutum 60 ne suka mutu a karamar hukumarsa. Sai dai adadi ne da mahukuntan Indonesia ba su tabbatar ba.