Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 05 16Article 450819

BBC Hausa of Sunday, 16 May 2021

Source: BBC

Abubuwan da Buhari zai tattauna da Macron a Faransa

Buhari ya tashi daga Abuja  a ranar Lahadi zuwa taron Afrika na kwana huɗu a Paris Buhari ya tashi daga Abuja a ranar Lahadi zuwa taron Afrika na kwana huɗu a Paris

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai gana da Emmanuel Macron a ziyararsa Faransa.

Cikin sanarwar da fadar shugaban Najeriya ta fitar ta ce shugaban zai tashi daga Abuja a ranar Lahadi zuwa taron Afrika na kwana huɗu a Paris.

Kuma Buhari zai gana da shugaban Faransa inda za su tattauna batutuwa da dama da suka shafi ƙasashen biyu.

Shugaban zai tafi tare da rakiyar ministocinsa na harakokin waje da kuɗi da lafiya da kasuwanci da saka jari da kuma mai ba shi shawara kan sha'anin tsaro Babagana Mohammed Monguno.

Me za a tattauna ?

Fadar shugaban Najeriya ta ce taron ya shafi tattalin arzikin kasashen Afrika da kuma tallafi ga ƙasashen sakamakon annobar korona.

Haka kuma zai yi duba kan yadda za a samu sassaunci musamman kan karuywar basukan da ake bin kasashen yankin.

Taron kuma wanda shugaba Macron zai jagoranta zai kunshi da masu ruwa da tsaki kan harkokin tattalin azrika a duniya da wasu shugabannin kasashe wadanda duka za su tattauna kan kudaden cikin gida da basuka da ake bin Afrika da kuma farfado da masana'antu masu zaman kansu.

Sannan Buhari zai keɓe da shugaban Faransa Emannuel Macron domin tattauna ƙaruwar barazanar tsaro a yankin Sahel da kuma Tafkin Chadi.

Kazalika za su tattauna kan alakar siyasa da ta tattalin azriki da sauyin yanayi da kuma hada hannu wajen bunkasa bangaren lafiya musamman gudanar da bincike kan yadda korona ke yaduwa da kuma samun rigakafinta.

Kafin Buhari ya dawo zai tattauna da masu ruwa da tsaki kan harkokin mai da iskar gas, da kuma kwararru a kan harkokin sadarwa.

Zai karbi bakuncin wakilan kungiyar tarayyar Turai kan harkokin kasashen ketare da tsare-tsare kan harkokin tsaro.

Buhari kuma zai gana da ƴan Najeriya mazauna kasar Faransa.