Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 05 29Article 451038

BBC Hausa of Saturday, 29 May 2021

Source: BBC

'Abin da ya sa muka hana makiyaya shiga Kano sai da izini'

Kano ta shirya sabon ka'idoji kan karbar Fulanin makiyayan da ke shigan jihar Kano ta shirya sabon ka'idoji kan karbar Fulanin makiyayan da ke shigan jihar

Rundunar 'yan sanda a Kano tace dukkan wasu Fulanin makiyayan da zasu shigo jihar sai sun sami takardar izini daga kwamishinan 'yan sandan jihar da suka baro.

Kwamishinan 'yan Sandan jihar Sama'ila Dikko yace duk wani bafilatanin da bashi da takardar izini daga 'yan sandan garin da ya fito ba, sai sun zasu zurfafa bincike kafin su barshi ya shiga jihar Kanon.

Sama'ila Dikko ya kara da cewa, fulanin sai sun nuna takardar shaida daga shugabanninsu, sannan ko da makiyayi ba shi da takardar za su yi bincike akan shi idan ba su gamsu da bayanan aka samu akan shi ba, to sai dai ya koma inda ya fito.

Matakin na zuwa ne adaidai lokacin da ake ci gaba da da samun karuwar fulanin dake kwararowa cikin kanana huikumomin dake makotaka da Jihohin Kaduna, Katsina da Jigawa.

''Mun fahimci cewa fulanin da za su shiga jihar Adamawa su na shiga da takardu daga shugabanninsu na Fulani, sukan ba su takardar cewa saboda hali na kiwo su na neman inda za su fi samun ciyawa da ruwa da sauransu.

Wasu kuma su na karbar takardar ne daga wajen 'yan sanda saboda sha'anin tsaro a kuma tabbatar da cewa ba barayi ba ne. Shi ya sa muma muka dauki wannan matakin domin sanin cewa ba barayin shanu ko 'yan ta'adda ne masu aikata laifi ba ne, domin magance matsalar tsaro da ake fama da ita a Najeriya,'' inji Sama'ila Dikko.

Jami'an tsaron sun zauna da shugabainin Fulanin wadan nan jihohi da kuma na cikin Kano dan sanar dasu halin da ake ciki tare da neman hadin kansu dan ganin an tabbatar da tsaro da zamana lafiya a fadin jihar ta Kano.

Karuwar rashin zaman lafiya da hare-haren da ake kai wa fulani makiyaya da ke kudancin Najeriya, na daga cikin dalilan da ya sa suke yin kaura zuwa arewacin kasar.