Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 04 20Article 450319

BBC Hausa of Tuesday, 20 April 2021

Source: BBC

Abin da ya sa gwamnatin Katsina za ta tura karnuka gadin makarantu

Gwamnan jihar Katsina Alhaji Bello Masari Gwamnan jihar Katsina Alhaji Bello Masari

Gwamntin jihar Katsina da ke arewacin Najeriya ta ce za ta tura karnuka domin aikin gadi a makarantun da ke fadin jihar.

Kwamishinan ilimi na jihar Dakta Badamasi Lawal Chiranci ya shaida wa BBC cewa jihar ta ware makudan kudade domin samar da tsaro a makarantun ciki har da kewaye su da kuma ajiye karnuka.

"Gwamnan jihar Katsina Alhaji Bello Masari ya ware zunzurutun kudi kimanin Naira miliyan 580 domin a gyara katangun makarantun da suka rushe, kuma a sanya waya a kewayen katangun, an kuma fitar da wata dabara ta samar da karnuka a kowacce makaranta.

Karnukan na iya shakar kamshin da ba su amince da shi ba, kuma da zarar karnukan sun yi haushi na wani abu da ba su amince da shi ba, masu gadi da dalibai da jami'an tsaro za su tabbatar da cewa akwai matsala a inda suka jiyo haushin wanda hakan zai taimaka matuka."

Sai dai bai bayyana adadin karnukan da za a girke a makarantun ba da kuma kudin da za a kashe wajen dawainiyarsu.

Ya kara da cewa bisa al'ada karnukan da ake da su a gidaje kan yi haushi a duk lokacin da suka ga bakuwar fuska, ko motsin da ba su amince da shi ba. Domin haka gwamnati ta ba da shawarar a tanadi karnuka a makarantu, wadanda suke da su sai su kara inganta su.

"Wadannan karnuka za su yi tasiri saboda ba a Najeriya kadai ake amfani da dabba a matsayin tsaro, misali akwai inda suke amfani da kwakwa, ko jakuna saboda dalili na tsaro," in ji Dakta Badamasi.

A cewarsa gwamnatinsu za ta fara bai wa dalibai ilimi kan tsaro, yana mai cewa "misali a lokacin da aka sace daliban makarantar kwana ta Kankara masu satar mutanen ne suka ce su dawo a lokacin da suka yi yunkurin tserewa, sai muke ganin da daliban na da ilimin tsaro da ba za a sace su da yawa kamar haka ba."

A watan Disambar bara ne 'yan bindigar suka kai hari a makarantar sakandaren ta maza zalla da ke garin Ƙanƙara da tsakar dare tare da yin awon gaba da dalibai kusan 500.

Kwanaki uku da sace daliban, kungiyar Boko Haram ta fitar da wani saƙon murya inda ta yi ikirarin cewa ita ce ta sace ɗaliban, abin da ya janyo ce-ce-ku-ce a ƙasar baki ɗaya.

Sai dai daga nisani gwamnatin jihar Zamfara da ke maƙwabtaka ta ce ta hada gwiwa da 'yan kungiyar Miyetti Allah wajen ceto daliban.

Sace-sacen dalibai domin neman kudin fansa na ci gaba da tayar da hankalin 'yan kasar, domin kuwa tun bayan lamarin da ya faru a Kankara an ci gaba da sace dalibai daga makarantunsu a wasu jihohin.