Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 05 28Article 451012

BBC Hausa of Friday, 28 May 2021

Source: BBC

Abin da majalisa ta gano a binciken kudaden Najeriya da aka sace

Hoton wata zaman yan majalisar Wakilan Najeriya Hoton wata zaman yan majalisar Wakilan Najeriya

Wani kwamitin wucin-gadi na Majalisar Wakilai a Najeriya na ci gaba da bincike kan makomar kuɗaɗe da kadarorin da aka sace tsakanin 2002 zuwa 2021 kuma hukumomin gwamnatin tarayya suka kwato.

Kwamitin dai ya gayyaci manyan jami'an gwamnatin tarayya ciki har da Ministan Shari'ah da shugaban hukumar yaki da masu yi wa arzikin kasa ta'annati EFCC da Babban Akanta na ƙasa don amsa tambayoyi a kan dukiyar.

Wani mamba a kwamitin binciken Hon Sada Soli ɗan Majalisar Tarayya ya fada wa BBC cewa akwai abubuwa da yawa da suke bincike a kai kuma sun fara gano asusun gwamnati da kudaden suke.

Ya ce an soma yin binciken saboda wani kudiri da aka gabatar a zauren majalisar wanda ya nemi a gudanar da bincike kan kudaden da kadarorin.

A cewarsa, babban akanta na kasar ya fada musu cewa ba zai yiwu a bude wani asusun ajiya na gwamnati ba tare da huruminsa ba - "akwai asusu da aka bude wadanda ma su bai sani ba". in ji dan majalisar.

Babban akantan a cewar dan majalisar, ya yi musu bayani kan kudaden da ake mayar wa jihohi saboda suna da alaka da jihohi tun da ba na gwamnatin tarayya bane.

Dan majalisar ya ce jami'in hukumar EFCC da ya bayyana gaban kwamitin ya nemi a ba shi dan lokaci saboda akwai wasu bayanai da kwamitin ya nema wanda bashi da su.

Ya ce mataki na gaba da za su dauka bayan kammala duka binciken shi ne gabatar da rahotonsu ga zauren majalisar wakilan sannan hukumar da ke da hurumi ta yi wani abu a kai.

Sai dai ya ce ba za su iya kayyade lokacin kammala binciken ba saboda "abin yana ta kara budewa, don abubuwa da yawa suna fitowa, sun fi karfin abin da ake tunani a baya".