Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 06 03Article 451132

BBC Hausa of Thursday, 3 June 2021

Source: BBC

ACF: Akwai siyasa a abin da ke faruwa da yan Arewa a Kudancin Najeriya

Kisan Ahmed Gulak a Imo State ne sanadiyyar masayin ACF Kisan Ahmed Gulak a Imo State ne sanadiyyar masayin ACF

Ƙungiyar tuntubar juna ta dattawan arewacin Najeriya ta ce akwai siyasa a hare-haren da ake kai wa ƴan arewa a Kudancin Najeriya.

Hakan ne ya sa ƙungiyar ta gargadi ƴan arewa da su yi kafa-kafa idan bulaguro ya kama su zuwa kudancin Najeriya, musamman yankin kabilar Igbo.

Kungiyar ta yi wannan gargadin ne ganin kisan da aka yi wa wani dan siyasa daga Arewa, wato marigayi Ahmed Gulak, wanda ya je aiki jihar Imo.

Senata Ibrahim Ida, shi ne mataimakin shugaban ƙungiyar na ƙasa kuma a hirarsa da BBC Hausa ya yi zargin kisan wani yunkuri ne na takalar fada da nufin wargaza Najeriya.

"Ana so ne a takalo mu inda har za mu ce mu dauki fansa saboda a ce mu muka sa kasar nan cikin kunci sannan mutanenmu ba mu gane inda aka nufa ba - dole sai mun yi bacci da idanunmu bude". in ji Ida.

A cewarsa, akwai siyasa a hare-haren da ake kai wa yan arewa a Kudancin kasar saboda a ganinsa zai yi wuya a ce abubuwa irin haka na faruwa a ce babu siyasa a ciki.

Ya ce akwai bukatar su fadakar da jama'a tun kafin lokaci ya kure.

Sanata Ida ya kara da cewa ana samun irin wannan ta'annati a duk lokacin da aka ce zabe ya kusa a kasar "za ka ga Najeriya kamar ba za ta kai gobe zuwa jibi ba".

Ya kuma zargi wasu yan siyasa da suke ba da gudummawa domin biyan bukatunsu na kashin kai.

A cewar Sanata Ida, matukar ana son a samu gyara a halin da ake ciki a Najeriya, toh dole ne yan kasa su bai wa gwamnati dukkanin goyon bayan da take bukata domin ita kadai ba za ta iya ba.