Vous-êtes ici: AccueilCultureMusique2021 04 23Article 450395

BBC Hausa of Friday, 23 April 2021

Source: BBC

An yi wa wasu mata-maza 'yan Kano tiyatar sauya jinsi a Sokoto

Gwamnatin Kano za ta gina cibiyar kula da masu fama da larurar mata-maza a jihar Gwamnatin Kano za ta gina cibiyar kula da masu fama da larurar mata-maza a jihar

Gwamnatin jihar Kano a arewacin Najeriya ta ce za ta gina cibiyar kula da masu fama da larurar mata-maza a jihar.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana hakan a yayin da yake karɓar ƴan asalin jihar maza da mata su shida da aka yi wa aiki a asibitin koyarwa na Jami'ar Sokoto a gidan gwamnati a ranar Laraba.

A lokuta da dama masu fama da wannan lalura kan gaza nema wa kansu lafiya ne saboda ɗawainiyar kuɗaɗen da ake kashewa kafin samun lafiya.

Gwamna Ganduje ya ce saboda ƙarancin likitoci da ke da ƙwarewa a wannan fannin a Kano, gwamnatinsa za ta haɗa gwiwa da cibiyar kula da masu lalurar mafitsara da ƙoda ta Jami'ar Usman Dan Fodio da ke Sokoto, don horarwa wajen kula da masu fama da wannan larura.

"Wannan ya zama dole ne a wuyan gwamnati domin a taimaka, saboda wannan al'amari ne da bayan ya shafi lafiyarsu ya kuma shafi hanyar rayuwarsu da tunaninsu. Za mu sa ɗamba domin gina wannan cibiya ta yi wa mata-maza aiki domin a warkar da su.

"Za mu ƙulla ƙawance tsakaninmu da Jami'ar Usman Dan Fodio domin ta koyawa likitocinmu da nas-nas da masu aiki a ɗakunan gwaji domin su naƙalci wannan aiki sosai da sosai," in ji Ganduje.

Gwamnan ya ƙara da cewa za su ci gaba da neman masu irin wannan lalura a jihar Kano "domin gwamnati ta taimaka ta biya kuɗaɗe a yi musu aiki kyauta har su warke."

Farfesa Isma'ila Arzika Mungadi, shi ne shugaban cibiyar kula da masu larurar mafitsara da ƙoda ta Jami'ar Usman Dan Fodio da ke sokoto, ya ce cikin yara bakwai da suka yi wa aikin, sun yi nasarar mayar da huɗu daga ciki mata, biyu kuma maza.

"Wasu daga cikin yaran sun fi ƙarfi ta gefen maza, wasu kuma ta gefen mata suka fi ƙarfi. Biyar daga cikinsu gefen mata ya fi ƙarfi, ɗaya kuma ya fi ƙarfi ta gefen maza.

"Duk sun warke kuma an kammala aikin amma ɗaya daga cikinsu zai dawo saboda shi an mayar da shi namiji ne bisa zaɓinsa, to sau biyu aka yi masa aikin don haka sai ya dawo mun duba ko abin ya yi kyau.

"Idan bai yi ba dole mu gyara don wani sa'in dama haka aikin yake," in ji likitan.

Sai dai ya jaddada cewa aikin yana da wahala sosai don a kan ɗauki dogon lokaci ana yi kuma wasu lokutan sai an yi kamar sau biyu ko uku.

Farfesa Mungadi ya ce baban ƙalubalen da suke fuskanta shi ne yadda masu fama da wannan lalura ke dagewa sai an bar su da halittar da aka san su da ita, saɓanin wadda suka fi ƙarfi akai.

Daukar nauyin yi wa masu fama da wannan larura ta mata maza da gwamnatin ta Kano ta yi, ya biyo bayan wata hira da BBC ta yi da wata mace ce mai laruruar mata maza, inda ta koka yadda tsangwama ta hana ta ci gaba da karatu.

Baya ga haka kuma a lokuta da dama masu fama da irin wannan larura da ma iyayen su kan sha tsangwama da gori, wanda a wasu lokutan sukan hakura da shiga mutane, kuma hakan kan shafi mu'amalar rayuwarsu ta yau da kullum.

To sai dai a wasu kasashe musamman wadanda suka ci gaba, hakan ba abin ɓoyewa ba ne ballantana a ce a yi wa mai lalurar gori, watakila saboda bambancin al'ada da fahimta da ci gaban fasahar zamani.