Vous-êtes ici: AccueilCultureMusique2021 03 17Article 449703

BBC Hausa of Wednesday, 17 March 2021

Source: BBC

Man United ta mata za ta yi wasa a Old Trafford a karon farko

United din za ta yi wasan ba 'yan kallo United din za ta yi wasan ba 'yan kallo

Kungiyar kwallon kafa ta mata ta Manchester United za ta buga wasa a Old Trafford a karon farko, tun bayan da aka kafa ta a 2018.

United din za ta karbi bakuncin West Ham United a gasar kwallon kafa ta mata ta Ingila ranar Asabar 27 ga watan Maris.

Kungiyar tana mataki na uku a kan teburi, kuma ba ta taba taka leda a filin da maza ke buga wasanninsu ba, wato Old Trafford.

United din za ta yi wasan ba 'yan kallo, saboda tsoron yada cutar korona, kuma a lokacin da maza ke buga wa tawagoginsu wasannni, shi ya sa ta samu wannan damar.

Filin wasan daya ne daga wadanda za su karbi bakuncin gasar kwallon kafa ta mata ta cin kofin nahiyar Turai da Ingila za ta karbi bakunci a 2022.

Manchester United ta mata na buga wasanninta a Leigh Sports Village tun bayan da ka kafa kungiyar shekara uku da ta wuce.

Sauran kungiyoyin kwallon kafa na mata kamar Manchester City da Chelsea da Tottenham da West Ham da Reading da Bristol City da Brighton da kuma Aston Villa, suna daga cikin akalla masu yin wasa a wurin da maza ke taka leda a karawar gida a kaka biyu da ta wuce.

A gasar bara Liverpool da Everton sun buga wasa na hamayya a Anfield da kuma Goodison Park.