Vous-êtes ici: AccueilSport2021 03 15Article 449648

BBC Hausa of Lundi, 15 Mars 2021

Source: BBC

Abia Warriors ta caskara Kano Pillars

Abia Warriors ta sharara kwallo 4-1 a ragar Kano Pillars a wasan mako na 15 Abia Warriors ta sharara kwallo 4-1 a ragar Kano Pillars a wasan mako na 15

Abia Warriors ta sharara kwallo 4-1 a ragar Kano Pillars a wasan mako na 15 a gasar Firimiyar Najeriya da suka kara ranar Lahadi.

Abia ce ta fara cin kwallo ta hannun Godwin Obaje minti 21 da fara tamaula, sai Obioma Chukwuemeka ya kara na biyu a minti na 34.

Minti hudu da aka ci Pillars kwallo na biyu ne ta zare daya ta hannun Nyima Nwagua.

Sai dai kuma Obioma Chukwuemeka ya kara na uku kuma na biyu da ya ci a karawar, sannan Daniel Wotlai ya zura na hudu a ragar Pillars saura minti bakwai a tashi.

Da wannan sakamakon Pillars ta koma ta hudu da maki 24, ita kuwa Abia Warriors tana ta 10 mai maki 20.