Vous-êtes ici: AccueilSport2021 05 10Article 450691

BBC Hausa of Lundi, 10 Mai 2021

Source: BBC

Waiwaye: Yunƙurin kifar da gwamnatin Buhari da Sakin ɗaliban kwalejin Kaduna

Shugaba Muhammadu Buhari Shugaba Muhammadu Buhari

Ga wasu daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a makon da ya gabata a Najeriya, daga Lahadi 1 ga Mayu zuwa Asabar 8 ga watan.

Yunkurin kifar da gwamnatin Buhari

Fadar shugaban Najeiya ta yi zargin cewa wasu tsoffin shugabannin siyasa da malaman addini suna yin markashiyar da za ta kai ga kifar da gwamnatin Muhammadu Buhari.

Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar Femi Adesina ya aike wa manema labarai ta ce mutanen suna son kawo yamutsi a kasar ne sanna su yi amfani da damar wajen kifar da gwamnatin.

"Ranar Lahadi Hukumar tsaron farin kaya ta (DSS), ta jawo hankali game da muguwar aniyar wasu da ke son hargitsa gwamnati da dorewar kasar.Wasu malaman addini da tsoffin masu rike da mukaman siyasa da da ba sa kishi ne suke gaba-gaba, kuma manufarsu ita ce daga karshe kasar ta fada cikin rikici, wanda zai tilasta sauya shugabancin zuwa wanda ba na dimokradiyya ba," in ji Mr Adesina.

Ya kara da cewa wasu hujjoji masu kwari sun nuna cewa wadannan mutanen suna daukar nauyin shugabannin wasu kabilu da 'yan siyasa a duk fadin kasar, bisa niyyar gudanar da tarukan da za su yi Allah-wadai da shugaban kasa, lamarin da zai kara jefa kasar cikin yamutsi.

Sakin 'yan matan kwalejin gandun daji

An saki sauran ɗaliban da aka sace na kwalejin Horar da Harkokin Noma da Gandun Daji ta gwamnatin tarayyya da ke Kaduna.

Ɗaya daga cikin iyayen ɗaliban ya tabbatar wa BBC cewa an saki ɗalibai 27.

Ya ce suna kan hanyar karɓar ɗaliban.

Shiekh Ahmad Abubakar babbam malamin addinin Islama da ke da'awar yin sulhu da ƴan bindiga ya shaida wa BBC cewa su shiga tsakani da aka saki ɗaliban.

"Mu muka yi ƙoƙarin ganin an sake su tare da taimakon tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo," in ji Sheikh Gumi.

Sai dai malamin bai bayyana cewa ko an biya kuɗin fansa ba kafin aka saki ɗaliban.

Dakatar da Hadiza Bala Usman

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin dakatar da shugabar hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta ƙasar, wato NPA, Hajiya Hadiza Bala Usman daga muƙaminta, domin a gudanar da bincike game da wasu kura-kurai da ake zargin ta da aikatawa.

An kuma umarci wani jami'i, Muhammadu Koko, ya riƙe muƙaminta, yayin da ake gudanar da binciken, wanda wani kwamiti da aka naɗa karkashin jagorancin darakta mai kula da sufurin jiragen ruwan a ma'aikatar sufuri ta ƙasar, zai gudanar.

Gwamnati ta ce ministan ma'aikatar sufuri ne ya nemi Shugaba Buhari ya ba shi izinin kafa kwamitin bincike don ya duba yadda ake gudanar da ayyuka a fannin jiragen ruwa na Najeriya wanda Hadiza Bala Usman ke shugabanta.

Ya kuma ce yayin da ake wannan bincike ya kamata a dakatar da ayyukanta har zuwa lokacin da za a kammala shi.

Sace daliban jami'a a Abia

Rahotanni daga jihar Abia da ke Kudu maso Gabashin Najeriya na cewa ƴan bindiga sun sace wasu ɗaliban jami'a da ba a san yawansu ba.

An yi garkuwa da daliban ranar Laraba - ranar da aka sako wasu dalibai 29 da aka sace a watan Afrilu a jihar Kaduna da ke Arewa maso Yammacin ƙasar bayan zargin an biya kuɗin fansa.

Mahukunta a birnin Umuahia sun ce ɗaliban jami'ar jihar Abia da ke Uturu na cikin wata mota ne lokacin da ƴan bindigar suka afka musu. An sace ɗaliban tare da wasu matafiya.

Wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai na jihar John Kalu ya ce biyu daga cikin ɗaliban sun tsere daga hannun masu garkuwar yayin da sauran kuma suke hannun ƴan bindigar a wani wuri da ba a gano ba.

Zabtare Albashin Ma'aikata

Gwamnatin Najeriya tana nazari kan albashin ma'aikata da kuma rage yawan hukumomi da ma'aikatun gwamnati.

Ma'aikatar kuɗi da kasafi da tsare-tsare ta ce an kafa kwamiti da zai yi nazarin yadda za a rage yawan kuɗaɗen da gwamnati ke kashewa musamman zabtare albashi da kuma rage yawan hukumomi.

An ambato ministar kuɗin Najeriya Zainab Ahmed na cewa, dole ne a fito da hanyoyin warware matsalar ƙarancin kuɗi da gwamnati ke ciki, lura da irin tsare-tsaren da ta ɗauko da kuma lalurorin yau da kullum da ta ke magancewa kamar albashi da sauran kuɗaɗen tafiyar da gwamnati.

Mai magana da yawun ma'ikatar kuɗin ta Najeriya Yunusa Tanko Abdullahi ya shaida wa BBC cewa gwamnati za ta yi aiki da shawarwarin rahoton kwamitin Oronsaye wanda tsohuwar gwamnatin Jonathan ta kafa.

Mutuwar Mama Taraba

Tsohuwar Ministar Mata ta Najeriya Hajiya Aisha Alhassan ta rasu.

Wata majiya ta shaida wa BBC cewa tsohuwar ministar ta rasu ne a wani asbiti da ke birnin al-Kahira na Masar bayan fama da wata gajeriayar rashin lafiya.

Marigayiyar wadda aka fi sani da 'Mama Taraba' ta rike mukamin Sanata mai wakiltar Taraba ta Arewa.

Ta yi takarar gwamnan Jihar Taraba a zaben 2015.