Vous-êtes ici: AccueilActualités2021 05 03Article 450561

BBC Hausa of Lundi, 3 Mai 2021

Source: BBC

'Yan sanda sun kama tarin makamai da alburusai a Jihar Ebonyi

Yan sandan sun kama tarin makamai da alburusai a Abakalki, a Jihar Ebonyi Yan sandan sun kama tarin makamai da alburusai a Abakalki, a Jihar Ebonyi

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce ta kama tarin makamai da alburusai a Abakalki, babban binin Jihar Ebonyi da ke kudancin Najeriya.

A wata sanarwa da kakakin rundunar Frank Mba ya fitar ranar Lahadi, ya ce an kama makaman ne a wata motar haya da ke kan hanyarta ta shiga Umuahia da ke jihar Abia.

Sanarwar ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano su wane ne ke da wadannan makamai da harsashi 753 da aka kwace.

A gefe guda kuma, 'yan sanda sun gano maboyar wasu mutane da ake zargi da aikata fashi a bankin Onueke ranar Talata 27 ga watan Afrilun da ya gabata a kauyen Oriuzo da ke Karamar Hukumar Ezza ta Arewa a jihar ta Ebonyi.

A cewar 'yan sanda, da ganin jami'an tsaro wadanda ake zargin suka bude musu wuta, nan da nan su ma 'yan sandan suka mayar da martani, inda suka kashe mutum uku - maza biyu da mace daya - sauran suka gudu.

An kwato bindiga kirar AK-47 guda biyu, ƙaramar bindiga guda shida, sai wadda ake girkewa guda biyar tare da harsashi 50. An kuma gano mota kirar Honda mai lamba ABJ 163 NV, in ji jami'an tsaron.

A baya-bayan nan masu fafutukar ballewa daga Najeriya sun matsa kaimi wajen kai hare-hare a kudu maso gabas da kudu maso kudancin kasar.

Ko a watan da ya gabata sai da 'yan ƙungiyar IPOB suka kai wa ofishin 'yan sanda hari tare da kai wani harin na daban kan gidan yarin Owerri a jihar Imo.

Sai dai jami'an tsaro na cea suna yin bakin kokarinsu wajen ganin an dakile wadannan muggan ayyuka a kasar.

A watan da ya gabata ne rundunar haɗin gwiwa ta musamman ta kashe wani babban kwamandan kungiyar IPOB a kudu maso gabashi, wanda ake kira da Ikonso tare da wasu mutum shida.