Vous-êtes ici: AccueilActualités2021 03 07Article 449520

BBC Hausa of Sunday, 7 March 2021

Source: BBC

Yadda ƴan bindiga suka sace ma'aikata da matansu a Kaduna

ƴan bindiga sun sace ma'aikata da matansu a Kaduna ƴan bindiga sun sace ma'aikata da matansu a Kaduna

Hukumomi a Najeriya sun ce suna gudanar da bincike don gano wasu mutane ciki har da mata da kananan yara da ake kyautata zaton 'yan bindiga ne suka sace su a jihar Kaduna.

Wayewar garin jiya ne 'yan bindigar suka kutsa gidajen kwananan ma'aikatan hukumar kula da filayen jiragen sama ta kasar, inda suka yi awon gaba da mutum goma ko da yake hukumar ta FAAN tace har kawo yanzu ba ta san adadin yawan mutanen ba.

Wata majiya da ta buƙaci BBC ta sakaye sunanta, ta ce maharan sun shiga rukunin gidajen ma'aikatan ne bayan lalata shingen wayar da ta kewaye filin sauka da tashin jiragen sama na jihar Kaduna, da wayewar garin ranar Asabar.

Majiyar ta ƙara da cewa daga nan ne suka shiga gidajen kwanan ma'aikatan, inda nan ma suka fasa katangar, sannan suka shiga wasu gidaje biyu.

''Sun faffasa kofar gida na farko, tare da tattara iyalan gidan wuri guda, ciki har da wasu baƙi da suka je ziyara, daga nan suka sake tsallakawa suka shiga wani gida tare da sace matar gidan da wasu yara, ko da yake mai gidan wanda bayanai suka nuna cewa ma'aikacin hukumar kula da yanayi ta Najeriya ne ya tsira, don baya nan a lokacin da al'amarin ya faru'' a cewar wannan majiya da muka zanta da ita.

Wasu rahotanni sun ce sai daf da tafiyar yan bindigar ne jami'an tsaro suka iso wajen, don haka basu kama kowa a cikinsu ba.

Ita dai hukumar kula da filayen sauka da tashin jiragen sama ta Najeriya ta tabbatarwa BBC faruwar wannan al'amari, amma ta ce ba a san adadin mutanen da aka sace ba, amma jami'an tsaro na ci gaba da gudanar da bincike.

Duk da kasancewar ba a samu rahoton rasa rai ba, ana zaton an samu raunuka, domin an ga jini a ƙofofin gida na farko da maharan suka shiga.

BBC ta yi ƙokarin jin ta bakin kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida a jihar Kaduna Samuel Aruwan, amma ya ce zai tuntube mu daga bisani saboda wani uzuri.

Jihar Kaduna dai na daya daga cikin jihohin Najeriya da suka fi fama da matsalar tsaro a halin da ake ciki, sai dai mahukunta sun sha cewa suna iya bakin ƙokarinsu don tabbatar da zaman lafiya a jihar.