Vous-êtes ici: AccueilActualités2021 03 22Article 449801

BBC Hausa of Monday, 22 March 2021

Source: BBC

Yadda kungiyar maza marowata a Najeriya ke jan hankali

Kungiyar maza marowata ya fara karbuwa a kafafen sada zumunta Kungiyar maza marowata ya fara karbuwa a kafafen sada zumunta

Matan Najeriya na kallon yadda mazan kasar suke zama tamkar 'yan tawaye.

Da yawansu ba sa iya bai wa ƴan matansu kuɗin toshi, wasu ba sa iya ba da kyaututtuka masu tsada, da yawa sun daina bai wa ƴan matan kyautar kudi don bukatunsu.

Wannan duk ya yi daidai da ra'ayin kungiyar maza marowata.

Wani kirkirarren ra'ayi ne - wanda ya fara karbuwa a wurin mazan kasar a kafafen sada zumunta a farkon wannan shekarar kan maganar ba da kuɗin toshi.

"Abu ne mai wuya kasancewa namiji a Najeriya, muna shan matsin lamba sosai," in ji wani dan jarida da ke zaune a Legas dan shekara 35.

"Kowa ya dogara a kanka. Bai kamata a rika kallon maza ba a matsayin saniyar tatsa ba, muna bukatar a rika girmama mu da ganin ƙimarmu."

Wani mutum a shafin Facebook ya ce yana ganin bai samu kimar da ya kamata ya samu ba ta ɓangaren ba da kudin toshi ba: "Mutane da yawa ana musu kallon na'urar ba da kudi saboda kawai suna da kirki."

Tashen da wannan kungiya ke yi a kafafen sada zumunta ya samar da wata manhaja da za a iya saukewa a tsara yadda katin shaida ya kamata ya kasance.

Cikin 'yan kwanaki an sauke wannan manhaja sama da 50,000.

"Akwai bukatar duk wani mamba ya yi rantsuwa kan cewa ko sisi ba zai bai wa mata ba.

Abin tamkar wani wasan kwaikwayo, amma abin ya ya wuce wasa, lamari ne kan yadda matasa a Najeriya za su rika fuskantar junansu a lokutan soyayya.

Soyayya a Najeriya yanzu tsada ne da ita.

"Na taba bayar da agogo na a madadin kudin da muka kashe"

Akwai wasu 'yan mata da suke dogara kan cewa 'yan mata ne za su biya kudaden bukatunsu na yau da gobe idan suna soyayya, kuma ba sauki ba ne da su.

Za su iya cewa a saya musu abubuwan zamani da ake yayi masu matukar tsada.

"Lokacin da ba ni da aure, na taba daukar wata budurwata muka je yawo na kashe mana kudi," in ji Mista Itua.

"Sun zo tare da kawarta suka ci abincin da ya fi karfin aljihuna. Ba ta nuna za ta biya ko sisi cikin kudin ba, dole haka na ba da agogo na domin biyan abin da muka kashe. Daga baya ma sai ta daina soyayya da ni."

Tunanin saduwa da budurwar da ake soyayya da ita na cikin tunanin mafi yawan maza, wanda wannan ce babbar matsalar da matan ke fuskanta daga mazan.

"Mafi yawan maza a kasar na da wannan manufar a zuciyarsu,"in ji Amarachi Kanu wata mai shekara 38 a Najeriya.

"Da yawansu suna kula mata ne da niyyar su kwanta da su.

"Mata na tambayarsu kudi ko kyauta ba wai dan a rika amfani da su ba ne."

Misis Kanu ta zargi maza da yadda suke mayar da mata su dogara a kansu.

"A kasashe da dama ba wani abin kunya ba ne mace ta biya kudin da suka ci abinci da saurayinta, amma a Najeriya mazan ne ke sanya mata jin ba sai sun biya kudi ba."

Ta ce tana matukar shan wuya a soyayya musamman lokacin da take neman biyan kudin da suka kashe.

"Ba ni da wani saurayi da ya taba biyan kudin abin da na saya tun asali, mace ce ni mai dogaro da kai.

"Wannan ya sa nake shan wuya wajen samun masoyi amma dai daga baya na samu miji na yi aure."

"Bai kamata soyayya ta zama kamar kasuwanci ba," ta kara da cewa.

'Wasu abubuwan da ake shiru a kansu lokacin soyayya'

Kwararriya kan halayyar dan adam Ann Uramu, ba ta yi aure ba lokacin da take farkon shekaru 20 na rayuwarta, amma kuma ta yi ta soyayya.

Sai dai babu abin da ya dame ta da wasu ka'idojinsu da ba a fada.

"A mafi yawan lokutan da nake soyayya idan muka fita da saurayi ya ce zai biya, kyale shi na ke, amma ina tabbatar da cewa in muka kara kashe kudi ni zan biya." in ji ta.

"Ina fara kare mutunci na ne ko da yaushe tun daga farkon alakarmu, kuma ba na soyayya da wanda ba zai iya fahimta ta ba.

"Ni mai bin addinin Kirista ce, kuma na yi amannar ana kwanciya ne kawai da mace lokacin da aka yi aure, Ba na yarda mutum ya kashe mani kudi sosai."

Kamata ya yi soyayya ta zama kashin bayan duk wata alaka, ta yadda za ka rika ganin soyayya a jikin wanda kuke soyayya.

Babu son kai a soyayya, don haka duka bangarorin biyu ya kamata su rika mutunta juna."

Misis Kanu ta yarda cewa idan da soyayyar gaskiya "kudi da kwanciya ba za su zama wasu abubuwa da za a rika magana a kansu ba".

Yanzu akwai jajurtattun mata. Da yawa suna daukar nauyin kansu har su taimakawa mazansu," in ji ta.

"Dan haka ba duka mata ba ne ke jiran maza su kashe musu kudi ba."