Vous-êtes ici: AccueilActualités2021 05 19Article 450858

BBC Hausa of Wednesday, 19 May 2021

Source: BBC

Chelsea ta rikito da Leicester zuwa ta hudu a Premier

Yan wasan kungiyar Chelsea Yan wasan kungiyar Chelsea

Chelsea ta yi nasarar doke Leicester City da ci 2-1 a wasan mako na 37 a gasar Premier da suka kara ranar Talata a Stamford Bridge.

Antonio Rudiger ne ya fara ci wa Chelsea kwallo, sannan Jorginho ya ci na biyu a bugun fenariti, yayin da Kelechi Ifeanacho ya farke wa Leicester daya.

Wannan shi ne wasa na uku da suka kara a tsakaninsu a bana, inda Leicester ta doke Chelsea 2-0 cikin watan Janairu, kuma wasa na karshe da Frank Lampard ya ja ragamar kungiyar.

Leicester City ta kuma doke Chelsea ta lashe FA Cup a karon farko ranar Asabar a Wembley.

Da wannan sakamakon Chelsea ta koma ta uku da maki 67, ita kuwa Leicester ta yi kasa zuwa mataki na hudu da tazarar maki daya tsakaninta da kungiyar Stamford Bridge.

Tuni dai kungiyar King Power ta samu gurbin Europa Leagu kai tsaye, bayan da ta lashe FA Cup na bana, illa tana kwadayin Champions League idan ta kare cikin hudun farko a bana.