Vous-êtes ici: AccueilActualités2021 04 23Article 450371

BBC Hausa of Vendredi, 23 Avril 2021

Source: BBC

Matan Saudiyya uku da suka zama jakadun kasar a kasashen waje

A tarihin Saudiyya, an taɓa naɗa mata uku a matsayin jakadu A tarihin Saudiyya, an taɓa naɗa mata uku a matsayin jakadu

A ranar Alhamis ne Inas Bint Ahmed Al-Shahwan ta sha rantsuwar kama aiki a gaban Yarima mai jiran gado Muhammad Bin Salman, a matsayin sabuwar jakadiyar Saudiyya a kasar Sweden, yayin wani biki da aka gudanar tare da sauran sabbin jakadun da aka nada.

Al-Shahwan ce mace ta uku a cikin matan Saudiyya da aka taɓa naɗawa a matsayin jakadu.

Naɗin nata ya biyo bayan na Gimbiya Reema Bint Bandar Bin Sultan da kuma Amal Bint Yahya Al-Moallimi.

A cikin watan Oktobar shekarar 2020 ne aka nada Amal Bint Yahya a matsayin jakadiyar Saudiyya a kasar Norway, inda ta zama mace ta biyu a kasar Saudiyya da ta taɓa riƙe irin wannan muƙami bayan Gimbiya Reema Bint Bandar.

Amma kuma, a cikin watan Afrilun shekarar 2019 ne aka rantsar da Gimbiya Reema a matsayin jakadiyar Saudiyya a Amurka, lamarin da ya bude wani sabon babi ga huldar diflomasiyyar Saudiyya.

Waɗannan naɗe-naɗe na nuni da gagarumin ci gaban da matan Saudiyya suka samu a fagen muƙamai masu martaba na jakadun kasashe, wanda galibi maza ne suka fi mamayewa.

Nade-naden wani bangare ne na shirin Vision 2030 na Masarautar Saudia, da ya ƙunshi ƙarfafa wa matan Saudiyya gwiwa.

Tun bayar kaddamar da shirin a cikin watan Afrilun shekarar 2030 ne matan kasar suka saku 'yancin tuka mota da kuma yin bulaguro ba tare da jagora namiji ba da dai sauran abubuwa.


Ga dai bayanai kan wadannan mata uku

Gimbiya Reema Al-Bandar

Ta gaji mahaifinta Bandar bin Sultan al-Saud, wanda ya riƙe mukamin jakadan Saudiyya a Amurka tun daga shekarar 1983 zuwa 2005.

Saboda wannan mukami ne ma ta yi mafi yawan rayuwarta a Amurka.

Ta yi digiri a fannin Ilimin Gidajen Tarihi daga Jami'ar George Washington.

Tun bayan komawarta birnin Riyadh a 2005, Gimbiya Rima ta yi aiki a ɓangaren gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu.

Ta riƙe muƙaman kasuwanci da dama da suka hada da shugabar kamfanin Harvey Nichols Riyadh.

Gimbiyar ta yi suna wajen fafutukar kare hakkin mata, a kasar da ake yawan sukart su da kuma rashin daidaiton jinsi.

A baya-bayan nan ta yi aiki a Hukumar Wasanni ta masarautar, da fatan mayar da hankali wajen ganin an sa mata cikin harkar wasanni da motsa jiki.

An kuma san ta da mayar da aiki tukuru wajen wayar da kai kan ciwon sankarar mama.

Wace ce Amal Bint Yahya Al-Moallimi?

Al-Moallimi ta kammala karatun digirinta na farko a fannin Turanci daga Jami'ar Princess Nourah bint Abdulrahman da ke birnin Riyadh.

Ta kuma yi karatu a kasar waje, inda ta yi digirinta na biyu a fannin sadarwa da kafofin yada labarai daga Jami'ar Denver da ke Amurka, da kuma wasu nazarin karatu daga Cibiyar Addinin Musulunci ta Oxford da ke Birtaniya.

Al-Moallimi ta fara aiki shekaru 23 da suka gabata a fannin harkokin ilimi, da horarwa da kuma kyautata jin daɗin jama'a.

Ta yi aikin koyarwa har na tsawon shekara biyar, kana ta yi aiki a sashen horarwa na ilmi na Ma'aikatar Ilimi a kasar.

Ta kuma yi aiki a matsayin mataimakiyar Sakatare Janar a Cibiyar Tattauna Al'amuran Kasa ta Sarki Abdul Aziz.

Jakadiyar ta kuma yi aiki a matsayin Janar Manaja ta kungiyoyin hadin kan kasa da kasa a Hukumar Kare Hakkin Biladama ta kasar Saudia (HRC).

Yayin da ta kara samun gogewa a fannin ayyuka na tsawon shekaru 20, Al-Moallimi ta riƙe muƙamai a fannonin ilmi da horarwa a fannin kyautata jin dadin jama'a.

Ta kuma ƙara samun ci gaba wajen riƙe babban matsayi na darakta janar na hukmomi da hadin ka kasa da kasa a Hukumar Kare Hakkin Biladama ta kasar Saudia (HRC) a shekarar 2019, inda ta zama mace ta shida cikin na farko da aka taɓa bai wa wannan mukamin.

Wace ce Inas Bint Ahmed Al-Shahwan?

A shekarar 2007 ne Al-Shahwan ta fara aiki da Ma'aikatar Harkokin Wajen Saudiyya.

Ta riƙe muƙamai a ma'aikatar, na karshe shi ne na mai bayar da shawara ga muƙaddashin ministan harkokin wajen kasar a fannin harkokin siyasa.

Ita ce kuma mace ta farko da ta taɓa riƙe mukamin manajan sashen harkokin siyasa da tattalin arziki a ma'aikatar harkokin wajen.

Har zuwa tsawon shekarun, Al-Shahwan ta shawo kan matsalolin muhimman abubuwan da suka shafi siyasa kana ta wakilci masarautar taruka da dama na yanki da kuma ƙasa da ƙasa.

Sabuwar jakadiyar ta kuma taimaka wajen horar da ma'aikata da dama na ma'aikatar harkokin wajen kasar da kuma maa'aikatan kasar a ma'aikatun gwamnati da dama.

Ta yi hakan ne ta hanyar gudanar da tarukan lakca da na bita a kan harkokin ƙasashen waje.

Al-Shahwan ta yi karatun digirin ta na biyu a fannin harkokin ƙasashen waje daga ƙasar Australia, kana ita mamba ce ta tawagar farko da ta kammala shirin horarwa na ''Future Leaders Program,", wanda ma'aikatar harkokin wajen ta ƙaddamar a shekarar 2017.

Ta kuma samu takardar shaidar a nazarin shugabanci daga Jami'ar Harvard.