Vous-êtes ici: AccueilActualités2021 04 23Article 450385

BBC Hausa of Friday, 23 April 2021

Source: BBC

Ku san Malamanku tare da Malam Muhammad Mashhood

Malam Muhammad Mashhud Malam Muhammad Mashhud



Shirin Ku San Malamanku na wannan makon ya tattauna ne da Malam Muhammad Mashhood, wani malamain addinin Musulunci a jihar Bauchin Najeriya.

An haifi Malam Muhammad Mashhood a garin Gusau na jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya.

Ya yi karatu a garin Maradi na jamhuriyar Nijar tun lokacin ya na dan shekara 7 da haihuwa.

A wancan lokacin bai damu da karatun Alkur'ani ba, alhalin shi ne aka kai shi ya yi, sai ya mayar da hankali a kan karatun littafan addini alhalin ba shi da tilawar ko izu biyar na Alkur'ani.

Bayan ya yi nisa a littafan Lugga sai ya karkato ya fara karatun Alkur'ani har ya yi saukar farko ya na da shekara 11.

Daga nan ne ya fara rubuta Alkur'ani, kuma a zamanin shi ne mafi kankantar shekaru da ya ke rubutun, wanda idan ya na yi har kewaye shi ake yi a cikin masallaci ana kallonsa.

"Sumuni ba ya shiga sumuni, rubu'i baya shiga rubu'i, nufsi ba ya shiga nufsi, hizifi baya shiga hizifi, ma'ana ya na rubutun kowanne takarda gud dya t na daukje fda sumuni daya.

"Duk da akwai sumuni masu tsawo a Ƙur'aNi ana tunanin ba za su shiga ba amma sun shiga," a cewar malam.

Ya rubuta Ƙur'aNi sun kai goma, duk littafin da ya karanta yana haddarsa, littafin farko da ya haddace na shi ne 'Burgatul Madi.

Bayan wannan ya haddace littafin Dandarani, da na Ishiriniya da kuma Diwani, da Nurul Basari da Wuturiyya da sauransu.

Malam Mashhood ya yi yawo sosai a kasar Saudiyya saboda yana da malamai a cikin Harami na Madina, da yake karatu a wajensu.

Abincin da Malamin ya fi ƙauna shi ne Indomie da ƙwai, ya kuma ce burinsa shi ne ya cika da kyau da imani.