Vous-êtes ici: AccueilActualités2021 04 17Article 450269

BBC Hausa of Samedi, 17 Avril 2021

Source: BBC

China ta samu bunkasar arziki mafi girma tun 1992

Tattalin arzikin China ya bunkasa da kashi 18 cikin dari a wata uku na shekara 2021 Tattalin arzikin China ya bunkasa da kashi 18 cikin dari a wata uku na shekara 2021

Tattalin arzikin China ya bunkasa da kashi 18 cikin dari a wata uku na farko na shekarar nan, waanda hakan wani gagarumin ci-gaba ne idan aka kwatanta da yadda ya kasance a bara.

Alkaluman da gwamnatin kasar ta China ta fitar sun nuna bunkasar tattalin arzikin ita ce mafi girma da aka gani tun 1992.

Wannan burunkasa ta tattakin arzikin na China ta kasance mai muhimmanci idan aka kwatanta da watanni uku na farko na shekarar da ta gabata 2020, lokacin da al'amura a kasar ta China suka tsaya cik saboda barkewar annobar korona.

Alkaluman hukumar kididdigar kasar sun nuna alama ta ci gaba da dorewar farfadowar tattalin arzikin, amma kuma tare da gargadin gagarumin rashin tabbas idan aka fadada ga kasuwancin kasar da sauran kasashen duniya.

Gwamnatin China ta yi kokarin shawo kan bazuwar cutar korona a cikin kasar cikin sauri.

Farfadowar tattalin arzkinta kusan ta wani fanni ya samu ne saboda matakin da gwamnati ta dauka na kashe kudi cikin gaggawa don tallafa wa masana'antu da kuma tabbatar da dorewar hakan.

To sai dai wannan ci-gaba da tattalin arzikin ya kasance kasa da yadda wasu masana tattalin arziki suka yi hasashe, inda su suka yi kiyasin zai kai kashi 19 cikin dari.

Kuma baya ga wannan ma, ana ganin alkaluman ba wata alama ba ce ta gagarumin ci gaban tattalin arzikin, saboda kwatanci da bara, lokaci ne da aka samu gagarumar durkushewa ta tattalin arzikin, wanda ya gamu da koma baya da kusan kashi bakwai cikin dari, saboda matakan kulle na korona.

Farfadowar tattalin arzikin dai ta dogara ne a kan fitar da kayayyaki waje, yayin da masana'antu ke ta ruguguwar samar da kayayyakin da aka saya daga gare su daga kasashen waje.

Wasu masana ma na ganin duk da cewa ana samun ci-gaba a sayen kayayayyaki a cikin gida, fannin ya samu nakasu sosai kuma yana ci gaba da kasancewa a baya-baya.

Bincike ya nuna duk da matsalar da aka samu ta koma bayan tattalin arziki a farkon shekara ta 2020, China ce wata babbar kasa mai karfin tattalin arziki da ta samu burunkasa a shekarar, ko da yake ta tsira ne da kashi 2.3 cikin dari, wanda wannan shi ne ci-gaba mafi rauni a gomman shekaru.

China ta sanya wa kanta burin cimma ci gaban tattalin arziki na kashi 6 cikin dari a wannan shekara ta 2021, bayan da ta rage buri a bara.

Daya daga cikin fitattun cibiyoyin tattalin arziki, OECD ta taba yin hasashe a 2012 cewa, za a samu wani gagarumin sauyi a duniya dangane da karfin arziki tsakanin kasashe zuwa shekaru hamsin.

Rahoton kungiyar ta OECD a lokacin ya ce, zuwa shekara ta 2016 China za ta shiga gaban Amurka ta fuskar karfin tattalin arziki.

Rahoton a wancan lokacuin ya kara da cewa a kasa da shekaru hamsin, tattalin arzikin kasashen China da India jimulla zai zarta na dukkanin kasashen da suka ci gaba.

Kungiyar ta OEDC ta kuma ce, kasashen da tattalin arzikinsu yake bunkasa za su shiga gaba.