Vous-êtes ici: AccueilActualités2021 04 20Article 450335

BBC Hausa of Tuesday, 20 April 2021

Source: BBC

Chelsea na shirin fita daga European Super League

Sama da magoya bayan Chelsea 1,000 sun taru a Stamford Bridge su nuna bacin rai da wannan shiri Sama da magoya bayan Chelsea 1,000 sun taru a Stamford Bridge su nuna bacin rai da wannan shiri

Kungiyar Chelsea na hada takardun da ta mika na neman izinin fita daga sabuwar gasar European Super League.

Wannan matakin ya zo ne kwana daya da aka sanar cewar Chelsea tana daga cikin kungiyoyi shida daga Premier League da suka amince su gudanar da sabuwar gasar.

A ranar Lahadi aka sanar da kungiyoyi 12 da ke shirin fara sabuwar gasar zakarun Turai, sai dai an yi ta caccakar wannan sabon yunkurin.

Sama da magoya bayan Chelsea 1,000 suka taru a Stamford Bridge kafin wasan da za ta kara da Brighton a Premier, inda suka nuna bacin rai da kungiyar ta fada wannan shirin.