Vous-êtes ici: AccueilActualités2021 04 20Article 450337

BBC Hausa of Tuesday, 20 April 2021

Source: BBC

Ed Woodward zai ajiye mukaminsa a Manchester United

Ed Woodward, babban mataimakin shugaban Manchester United Ed Woodward, babban mataimakin shugaban Manchester United

Ed Woodward zai ajiye aikin babban mataimakin shugaban Manchester United a karshen kakar 2021.

Hakan ya biyo bayan rashin amincewa da sabuwar gasar European Super League, wadda United tana daga cikin kungiyoyi shida daga Ingila da suka amince da tsarin.

Sauran daga Ingila sun hada da Arsenal da Liverpool da Manchester City da Chelsea da kuma Tottenham.

Sai dai tuni Manchester City ta sanar ranar Talata cewar ta fita daga tsarin buga sabuwar gasar ta European Super League, Chelsea ma za ta yi hakan.

Sauran kungiyoyi shidan da suke cikin tsarin sabuwar gasar har da Real Madrid da Barcelona da Atletico Madrid da Juventus da AC Milan da kuma Inter Milan.

Woodward, mai shekara 49 yana kan mukaminsa a Manchester United tun 2012.