Vous-êtes ici: AccueilActualités2021 04 20Article 450315

BBC Hausa of Tuesday, 20 April 2021

Source: BBC

An sauya fasalin gasar Champions League ta Turai

An amince da sabon fasalin gasar Champions League ta Turai An amince da sabon fasalin gasar Champions League ta Turai

An amince da sabon fasalin gasar Champions League ta Turai mai dauke da kungiyoyi 36 ranar Litinin.

Hakan ya zo kwana daya da kungiyoyi 12 har da fitattu shida daga Ingila da suka sanar da shirin fara sabuwar gasar kwallon kafa ta European Super League.

Wannan sabon fasalin da aka yi wa Champions League mai dauke da takaddama, zai fara aiki daga kakar 2024 zuwa karshen kakar 2033.

Tun a watan jiya wannan shirin ya ci karo da cikas, bayan da aka yi takaddama kan rawar da kungiyoyin za su taka wajen gudanar da gasar.

Wannan sabon tsari mai dauke da kungiyoyi 36 za su buga fafatawa goma-goma a zangon farko.

Hakan zai samar da teburin kungiyoyin da takwas din farko za su kai zagaye na biyu, daga nan sai kungiyoyi 16 sai zuwa Quarter finals da wasan daf da karshe da fitar da gwani.

Wannan tsarin ya ci karo da suka a wajen magoya baya, saboda biyu daga cikin gurbi hudun da za su buga gasar za a zabo ne bisa kwazon da suka yi a baya, ko wadanda ke kan gaba a fanni tamaula a jadawalin hukumar kwallon Turai.

Da tsarin ya fara aiki a yanzu a kakar nana, Liverpool duk da za a yi duba kan yadda za ta karkare a gasar Ingila tare da Chelsea su ne za su ci gajiyar shirin.

Sai dai ana ta caccakar wannan sabon fasalin, domin zai shafe tsarin zuwa gasar Champions League iya kwazonka a gasar kasa, zai koma har da wadda ta kasa taka rawar gani za ta iya zuwa gasar ta Zakarun Turai koda ta karshe ta yi a teburi.