Vous-êtes ici: AccueilInfos du MondeSport2021 03 14Article 449634

BBC Hausa of Sunday, 14 March 2021

Source: BBC

Chelsea ta kasa hawa na uku a Teburin Premier

Chelsea ta buga wasa na sha biyu ba a doke ta ba Chelsea ta buga wasa na sha biyu ba a doke ta ba

Mai horar da Chelsea Thomas Tuchel ya buga wasa na sha biyu ba a doke shi ba, biyo bayan tashi 0-0 tsakanin Chelsea da Leeds United.

Mai tsaron ragar Chelsea Eduoard Mendy ya haska sosai a wasan, bayan da ya tare kwallaye masu hatsari da suka hana Leeds cinye wasan a gida.

Sai dai kuma kasa cin wasan da Chelsea tayi ba labari mai daɗin ji bane ga Thomas Tuchel, a yunƙurin ƙungiyar na kakkaɓo Leicester City dake zaune na uku kan teburin Premier League.

Tunda farko Leeds United ta fuskanci cikas, bayan da ɗan wasan gabanta Patrick Bamford ya samu rauni kafin zuwa hutun rabin lokaci a wasansa na 100 da ƙungiyar.

A yanzu Leeds United za ta je gidan Fulham ranar Juma'a, yayin da Chelsea ke shirin karɓar bakuncin Athletico Madrid a gasar zakarun Turai ranar Laraba.