Vous-êtes ici: AccueilInfos du MondeGeneral2021 05 10Article 450688

BBC Hausa of Lundi, 10 Mai 2021

Source: BBC

An kubutar da 'mutum 30 cikin 40' da aka sace suna Tahajjud a Katsina

Jihar Katsina na Arewa maso yammacin Najeriya Jihar Katsina na Arewa maso yammacin Najeriya

Rundunar yan sandan Jihar Katsina da ke Arewa maso yammacin Najeriya ta ce ta yi nasarar kubutar da kimanin mutum 30 cikin 40 da yan bindiga suka sace a wani sabon masallaci da ke karamar hukumar Jibiya.

Kakakin rundunar yan sandan, SP Gambo Isah ya fada wa BBC cewa lamarin ya faru da tsakar daren ranar Litinin inda yan bindiga da ba za a iya tantance yawan su ba dauke da makamai da bindiga kirar AK47 suka kutsa cikin sabon masallacin da ke Unguwar Kwata.

A cewarsa, "lokacin da suka je sun yi harbe-harbe a sama kuma sun saci masallata wadanda suka fito domin yin sallar Tahajjud".