Vous-êtes ici: AccueilInfos du MondeGeneral2021 05 11Article 450722

BBC Hausa of Tuesday, 11 May 2021

Source: BBC

Ko Mbappe zai ci gaba da wasa a PSG kamar Neymar?

Kylian Mbappe tare da Neymar Jnr Kylian Mbappe tare da Neymar Jnr

Kawo yanzu an san makomar Neymar a Paris St Germain, bayan da ya tsawaita kwantiragin ci gaba da taka leda a kungiyar zuwa 2025.

Kawo yanzu an kawo jita-jitar da aka dade ana yi cewar zai sake komawa Barcelona ko kuma Real Madrid da zarar yarjejeniyar ta kare a 2021/22.

Yanzu dai hankali ya koma kan Kylian Mbappe a Paris St Germain, inda wasu ke cewar zai bar Faransa da taka leda, wasu kuma ke cewar zai ci gaba da wasa a kungiyar.

Tuni dai PSG ta yi wa Mbappe tayin kwantiragi mai tsoka, sai dai kawo yanzu dan kwallon tawagar Faransa bai kulla yarjejeniya ba.

Real Madrid tana daga cikin kungiyoyin da ke son daukar Mbappe tun yana Monaco kafin ya koma PSG, sai dan kwallon zai so ya san da makomar Zinedine Zidane ko zai ci gaba da horar da Real?

Shi dai Mbappe ya sha fada cewar yana son yaga tsare-tsaren da kungiyar ta tanada, kafin ya amince ya rattaba hannun kan kwantiragi.

Dan wasan ya fayyace cewar yana son lashe Champions League fiye da komai a fanni tamaulla, kuma damar da yake da ita tana PSG.

Sai dai matsin tattalin arziki da cutar korona ta jefa manyan kungiyoyin Turai da batun kirkirar gasa ta European Super League da Real ke jagoranci ya sa ba za ta samu kudin sayen dan kwallon a yanzu.

Watakila ta jira yarjejeniyarsa idan ta kare a karshen kakar 2021/22 ta dauke shi a matakin wanda bai da wata kungiyar, kuma cikin sauki da arha.

Manchester City ta fitar da PSG a wasan daf da karshe, kamar yadda Chelsea ta yi waje da Real a gasar Zakarun Turai, sai dai kungiyar ta Faransa ta buga wasan karshe a bara, inda Bayern Munich ta lashe kofin da ci 1-0.

Bayan da PSG ta dade da yin kaka gida a gasar Ligue 1, kungiyar ta kuma fasa cikin gasar Turai har ta kai cewar ta yi fice ana kuma tsoron haduwa da ita.

Ita kuwa Real Madrid wadda kakar bana ba ta dauki dan wasa koda daya ba, karsashinta na dakushewa.

Haka kuma bayan da Neymar ya amince zai ci gaba da taka leda, hakan zai bai wa Mbappe kwarin gwiwar amincewa ya ci gaba da zama a Paris St Germain domin kara bunkasa kungiyar a wasanninta a Turai da duniya.