Vous-êtes ici: AccueilInfos du MondeGeneral2021 05 24Article 450914

BBC Hausa of Monday, 24 May 2021

Source: BBC

Buhari da Osinbajo na shan suka kan kin halartar jana'izar sojoji

Lokacin da Buhari da Osinbajo suka kara wa Attahiru daraja a Janairu 2021 Lokacin da Buhari da Osinbajo suka kara wa Attahiru daraja a Janairu 2021

Ƴan Najeriya sun sako Shugaba Muhammadu Buhari a gaba da mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo musamman a Twitter saboda rashin halartar jana'izar Babban Hafsan sojin ƙasa da sojoji 10 da hatsarin jirgin sama ya kashe a Kaduna.

A ranar Asabar a Abuja aka binne Babban Hafsan sojin Najariya Janar Attahiru tare da sojoji 10 da suka mutu a hatsarin jirgin ƙasa a ranar Juma'a yayin wata ziyarar aiki daga Abuja zuwa Kaduna.

Sojojin da suka mutu sun ƙunshi Janar guda uku da suka haɗa da Birgediya Janar Kuliya babban jami'in leƙen asiri na sojin Najeriya da Birgediya Janar M Abdulkadir da kuma Birgediya Janar Olayinka.

Tun a ranar Juma'a da hatsarin jirgin saman ya faru fadar shugaban Najeriya ta fitar da sanarwa da ke cewa "Buhari ya yi matuƙar kaɗuwa game da hatsarin jirgin saman da ya yi sanadin mutuwar babban hafsan sojan ƙasa Janar Ibrahim Attahiru da kuma wasu jami'an soja.

Buhari, wanda ministan tsaro Janar Bashir Magashi (mai ritaya) ya wakilce shi wurin jana'izar sojojin, ya yaba wa Janar Attahiru kan jajircewarsa a yaƙin da yake jagoranta da masu tayar da ƙayar baya tare da bayyana shi a matsayin "Babban hafsan soji kuma jagoran da ake kwaikwayo da shi.

Duk da wasu manjan jami'an gwamnati da gwamnoni sun halarci jana'izar sojojin amma rashin halartar Buhari ne ya fi jan hankalin ƴan Najeriya.

Wasu na ganin mutuwar sojoji babban al'amari ne a Najeriya, kuma rashin halartar shugaban ƙasa da mataimakinsa ya nuna rayuwar sojojin ba komi ba ne.

Wasu kuma masu mayar da martani na bayar da dalilai na tsaro da annobar korona a matsayin abin da ya sa shugabannin suka ƙauracewa wurin jana'izar sojojin yayin da kuma wasu suka ce ba saɓa doka ba ne don shugaba bai halarci jana'iza ba.

Wasu kuma na ganin mahawarar da ake ba ta da wani amfani, abin da ya fi amfani ga ƴan Najeriya shi ne jimami da kuma yi wa ƙasa addu'a kan wannan babban rashin sojojin da aka yi.

Abin da ƴan Najeriya ke cewa

An yi ta tafka mahawara a Twitter kan rashin halartar Buhari a matsayinsa na Babban Kwamandan sojojin Najeriya da mataimakinsa wurin jana'izar sojojin da suka mutu inda ƴan Najeriya da dama ke suka da caccakar shugabannin.

Sunan Babban Kwamandan sojojin Najeriya C-in-C da Buhari da Osinbajo da Janar Attahiru sun kasance waɗanda aka fi tattaunawa a Twitter a Najeriya.

Kawo yanzu an yi amfani da sunan C-in-C fiye da dubu 116, an kuma yi amfani da sunan Buhari kusan sau dubu 60 yayin da kuma aka yi amfani da sunan Osinbajo fiye da 6,000.