Vous-êtes ici: AccueilMonde2021 05 19Article 450870

BBC Hausa of Mercredi, 19 Mai 2021

Source: BBC

Ordinary President: Mai shirin Brekete Family Ahmed Isah na shan yabo da suka ga ƴan Najeriya

Ahmed Isah, mai rajin kare haƙƙi a Najeriya da ke taimaka wa mutane wajen neman haƙƙinsu Ahmed Isah, mai rajin kare haƙƙi a Najeriya da ke taimaka wa mutane wajen neman haƙƙinsu

Binciken ƙwaƙwaf na BBC Africa Eye kan shirin Brekete Family ya ja hankalin ƴan Najeriya inda suka bayyana ra'ayoyi mabambanta kan wani ɓangare game da shirin da binciken ya gano.

Ahmed Isah, mai rajin kare haƙƙi a Najeriya da ke taimaka wa mutane wajen neman haƙƙinsu a rediyo da talabijin, ya sha yabo da suka sakamakon bidiyon BBC da ya nuna shi yana marin wata mace.

Ahmed wanda aka fi sani da 'Ordinary President' wato 'Gamegarin Shugaban Ƙasa', ya shahara ne sakamakon shirin da yake gabatarwa mai suna "Berekete Family" a gidan rediyon Human Rights Radio da ke Abuja, babban birnin Najeriya.

An gan shi yana zabga wa wata mace mari cikin wani bidiyon binciken ƙwaƙwaf na BBC Africa Eye, wadda aka zarga da cinna wa wata ƙaramar yarinya wuta a kanta bisa zargin cewa mayya ce yayin da yake tsaka da gabatar da shirin.

Ya zuwa yanzu, Ordinary President bai mayar da martani ba game da abin da aka gan shi yana aikatawa bayan sakin bidiyon.

Tun bayan wallafa bidiyon ne 'yan Najeriya suka dinga bayyana mabambantan ra'ayoyi, inda wasu ke ganin a matsayinsa mai kare haƙƙi bai kamata ya ci zarafin wani ba, wasu kuma na cewa "ta cancanci fiye da haka".

Abin da 'yan Najeriya ke cewa Tun farko, da BBC ta tambayi Ahmed Isah dalilin da ya sa ya mari matar yayin da ake ɗaukarsa a bidiyo, sai ya ce: "Na yi hakan ne domin na yi amfani da bidiyon da zummar koya wa mutane darasi".

Sai dai batun ya raba kan dubban 'yan Najeriya inda suka bayyana ra'ayoyi masu karo da juna a Twitter.

An yi amfani da 'Ordinary President' sau 17,500 ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, an kuma yi amfani da 'Ahmed Isah' sau 3,448.

"Ordinary President ya yi daidai. Ni kaina wallahi haka zan yi," a cewar wata mai suna petty patootie (@neptracy).










Abin da ake zargin matar da aikatawaKamar yadda bidiyon ya nuna, an kawo yarinyar ce 'yar shekara shida cikin zauren gabatar da shairye-shiryen na Brekete Family bisa zargin cewa wata 'yar uwar mahaifinta ce ta saka kalanzir kuma ta kunna mata wuta a kai.

Nan take Ahmed Isah ya kira kwamishinan 'yan sanda na birnin Abuja kuma cikin ƙasa da awa ɗaya suka isa wurin. Kazalika, ya yi alƙawarin ba ta tallafin kusan naira miliyan biyu.

Bayan bincike, an kama wadda ake zargin.

Ordinary President ya nemi a kawo matar domin yi mata tambayoyi. Sai dai ganin cewa ta kasa amsa masa tambayoyin game da dalilin da ya sa ta aikata abin da ake zarginta da shi, sai ya zazzabga mata mari fiye da sau ɗaya.

Kamar yadda rahoton ya nuna, yarinyar na ci gaba da samun kulawar likitoci a asibiti bisa tallafin kuɗin da Ordinary President ya tara mata, wanda da ma abin da yake yi kenan a cikin shirin nasa na Brekete Family.