Vous-êtes ici: AccueilMonde2021 05 25Article 450945

BBC Hausa of Mardi, 25 Mai 2021

Source: BBC

Marigayi Attahiru Ibrahim: Tarihin babban hafsan hafsoshin sojin da ya mutu a hatsarin jirgin sama

Babban hafsan sojojin ƙasa na Najeriya, marigayi Manjo-Janar Attahiru Ibrahim Babban hafsan sojojin ƙasa na Najeriya, marigayi Manjo-Janar Attahiru Ibrahim

Babban hafsan sojojin ƙasa na Najeriya, marigayi Manjo-Janar Attahiru Ibrahim, ya dare kan wannan mukami ne a watan Janairu.

Amma wata huɗu bayan ya kama aiki hatsarin jirgin sama ya rutsa da shi a filin jirgin sama na Kaduna, inda ya rasa ransa tare da wasu manya da ƙananan hafsoshin sojin ƙasar.

Kakakin rundunar sojin ƙasa na Najeriya, Birgediya-Janar Yerima Mohammed ya tabbatar wa BBC mutuwar babban hafsan sojojin kasan cikin wata sanarwa da rundunar sojojin kasa ta fitar.

Kafin mutuwarsa, Manjo-Janar Attahiru Ibrahim ne ke jagotrantar yaki da masu tayar da kayar baya a Najeriya, amma waye shi?

An haifi marigayi Attahiru Ibrahim a ranar 10 ga watan Agustar 1966.

Shi dan asalin ƙaramar hukumar Kaduna ta Arewa ne ta jihar Kaduna, kuma ya halarci makarantar horas da hafsoshin soji ta Nigerian Defence Academy da ke Kaduna, inda ya zama cikin ajin hafsoshin da su ka haarci kwalejin na 35.

Marigayin ya kammala karatunsa a kwalejin da aka fi sani da NDA, da kuma Armed Forces Command Staff College, da ke Jaji har ma da kwalejin da ke horas da ƙananan hafsoshin sojin kasa mai suna Nigerian Army school of Infantry dukkansu a jihar Kaduna.

An fara horas da shi ne a NDA a watan Janairun 1984, inda ya fito da mukamin Second Lieutenant a watan Disambar 1986 a matsayin cikakken hafsan sojan Infantry wato na ƙasa.

Ya kuma tafi jami'oi domin ƙaro ilimi, domin yana da digiri na biyu wanda shi ma ya samo shi daga kwalejin Nigerian Defence Academy ta Kaduna.

Yana kuma da wani digirin na biyu wato Masters daga Salford University da ke Birtaniya ban da wata Diploma da ya samo a Jami'ar Nairobi da ke kasar Kenya.

Marigayi Attahiru ya rike mukamai na soja masu dama yayin da ya ke raye.

Ya kuma sami damar tafiya zuwa Saliyo cikin tawagar Majalisar Dinkin Duniya a matsayin mai sa ido.

Manjo Janar Ibrahim Attahiru shi ne ya maye gurbin Janar Tukur Buratai babban hafsan sojan ƙasa.

Kafin ba shi muƙamin babban hafsan sojin kasa na Najeriya, Manjo-Janar Attahiru shi ne shugaban runduna ta 82 a rundunar sojin ƙasar.

Ya taba jagorantar yaƙi da ƙungiyar Boko Haram amma a shekarar 2017 ne Janar Tukur Buratai ya sauke shi daga muƙamin bayan wasu hare-hare da 'yan bindiga suka kai inda aka kashe wasu mutane 50 a lokacin da suke sallah a masallaci.

Janar Nicholas Rogers ne ya maye gurbinsa.