Vous-êtes ici: AccueilActualitésRégional2021 05 18Article 450851

BBC Hausa of Mardi, 18 Mai 2021

Source: BBC

Kudancin Najeriya : INEC ta kira taron gaggawa kan hare-haren da ake kai wa ofisoshinta a yankin

Shugaban INEC, Prof Mahmood Yakubu Shugaban INEC, Prof Mahmood Yakubu

Matsalar tsaro ta sa hukumar zaben Najeriya kiran wani taron gaggawa na jami'anta da ke jihohi, da na wani kwamitin musamman kan harkokin tsaro, bayan hare-haren da aka kai wa wasu ofisoshinta a yankin kudu maso gabas.

Hari na baya bayan nan da aka kai wa ofisoshin hukumar zaben shi ne wanda aka kai kan ofishinta da ke jihar Enugu, har ta kai an kona shi kurmus.

Daraktan wayar da kan jama'a na hukumar ta INEC Mista Nick Dazeng, ya shaida wa BBC cewa irin wannan hari shi ne na uku da aka kai wa hukumar, abin da ke janyo barazana ga zabukan 2023.

''Mun shaida wa jami'an tsaro dukkanin abubuwan da ke faruwa game da hare-haren da ake kai wa ofisoshinmu domin su gudanar da bincike don gano ko su wane ne suke yin wannan ta'asa, sannan ranar Larabar nan za mu gana da shugabannin hukumar zabe don tattauna batun'' in ji Dazeng.

Ya kara da cewa kafin karshen makon nan da ake ciki hukumar za ta kara zaunawa da kwamitin tsaro na Najeriya domin lalubo mafita game da al'amarin.

A dai dai lokacin da wannan ke faruwa rahotanni daga jihar Abia na cewa 'yan bindiga sun kutsa wani ofishin 'yan sanda tare da yin kaca-kaca da shi a Umuahia babban birnin jihar.

A jihar Anambra ma sakamakon yawan kai hare-hare da 'yan bindiga ke yi mahukunta sun sanar da sanya dokar hana fita a wasu kananan hukumomin jihar ta dare don kare rayuka da dukiyoyin jama'a.

Mai magana da yawun 'yan sandan jihar DSP Nkenga Chochkuwu, ya ce an kuma kafa dokar hana amfani da bakaken gilasan mota saboda yadda aka gano cewa bata gari na amfani da su wajen buya su kai hare-hare.

Akwai dai dubban sojoji da 'yan sanda da aka jibge a kudancin Najeriyar da zummar samar da zaman lafiya yayin da hare haren da ake zargin yan aware da kaiwa ke kara ta'azzara.