Vous-êtes ici: AccueilActualitésRégional2021 03 16Article 449692

BBC Hausa of Tuesday, 16 March 2021

Source: BBC

Enugu: Yadda kudirin biyan gwamnoni da matansu fansho ya haifar da ce-ce-ku-ce a Najeriya

Biyan gwamnoni da matansu fansho ya haifar da ce-ce-ku-ce a Enugu Biyan gwamnoni da matansu fansho ya haifar da ce-ce-ku-ce a Enugu

Majalisar Dokokin Jihar Enugu ta jingine wani ƙudirin dokar fansho na tsofaffin gwamnoni da mataimakansu da matansu wanda ya haifar da ce-ce-ku-ce a kafofin sada zumunta da kuma zanga-zanga.

Matakin ya biyo bayan suka da ƙalubalantar kudirin da jama'a suka yi a ranar Talata kan kuɗirin da ke neman biyan tsoffin gwamnonin da mataimakansu da matansu biliyoyin naira a matsayin fansho na har tsawon rai.

Haka kuma an nuna hotunan wasu mutanen Enugu a kafofin sada zumunta suna gudanar da zanga-zanga domin adawa da kudurin dokar.

Jaridar Cable ta ce ta samu kwafi na kudirin dokar kuma a ciki ta ga an yi wa gwamnoni ƙari da kusan kashi 900 na abin da za su dinga ƙarba duk shekara idan sun sauka.

Kudirin kuma a cewar jaridar ya shafi biyan matan tsoffin gwamnonin na jihar Enugu kuɗaden alawus duk shekara da suka kai kusan naira miliyan 12.

Batun wanda ya ja hankali da haifar ce-ce--ku-ce da zanga-zanga ya tilasta wa majalisar dokokin jihar fitowa ta bayyana cewa ta jingine kudirin.

An nuna hoton bidiyon shugaban Majalisar dokokin jihar ta Enugu yana yi wa masu zanga-zanga a harabar majalisar jawabi.

A cikin bidiyon an ji shugaban majalisar Edward Uchenna Ubosi yana cewa yanzu suka jingine kuɗirin

"Ku bari mu yi nazari kan kudurin, karatu na farko kawai aka yi bayan gabatar da shi. sai mun diba mun ga abin da za mu cire ko mu ƙara," in ji shi.

Me ake cewa?



Ƴan Najeriya da ke tsokaci a Twitter na ganin ya kamata gwamnati da ƴan majalisar Enugu su mayar da hankali kan ayyukan ci gaban al'umma amma ba azurta gwamnoni ba.