Vous-êtes ici: AccueilActualitésPolitique2021 05 17Article 450837

BBC Hausa of Monday, 17 May 2021

Source: BBC

Rikicin Isra'ila da Falasɗinawa: Masana na ganin babu ƙasar da za ta iya hana Isra’ila kai hare-hare

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce sojojin Isra'ila za su ci gaba da ɗauki-ba-daɗin da suke yi a Zirin Gaza "iya ƙarfinsu".

Hukomomin lafiya a Gaza sun ce mutum 200 ne suka mutu, ciki har da mata 16 da ƙananan yara 10, a hare-haren Isra'ila na baya-bayan nan ta sama.

Kazalika, an kashe mutum 10 ciki har da ƙananan yara biyu a hare-haren roka kan Isra'ilar waɗanda ƙungiyar Hamas ke kai wa tun ranar Litinin, 10 ga watan Mayu.

Ƙasashe da ƙungiyoyi daga sassan duniya na ta kiran da a tsagaita wuta.

'Babu wata barazana da za ta dakatar da Isra'ila daga kai hari'

A hare-hare mafiya muni da ta kai da asubahin Litinin, Isra'ila ta ce ta hari maɓoyar ƙarƙashin ƙasa mallakar ƙungiyar Hamas, amma an lalata tituna da wutar lantarki.

Wani mazaunin Daular Larabawa wato UAE kuma mai sharhi kan al'amuran Gabas ta Tsakiya, Muhammad Kaddam Siddiq Isa ya faɗa wa BBC cewa babu wata barazana da za ta sa Isra'ila ta dakatar da hare-hare a kan Falasɗinawa.

"Idan ana tunanin akwai wanin abu ko barazana da ƙasashen duniya za su yi wa Isra'ila ta daina kai hare-hare, amsa ita ce babu," in ji shi.

"Kawo ƙarshen wannan ya danganta da abin da su hukumomin Israi'la suka yanke cewa ya kamata su dakata, saboda babu wanda yake juya ta a halin yanzu."

Muhammad Ƙaddam ya ce yunƙurin da wasu hukumomi ke yi na shiga tsakani ba kowanne ne ke da tasiri ba.

"Yunƙurin da Majalisar Ɗinkin Duniya ke yi na sasantawa ba wani tasiri zai yi ba sosai, gara ma wanda ƙasar Masar take yi," a cewarsa.

"Wakilan Masar na Gaza yanzu haka kuma suna ƙoƙarin tattaunawa da ɓangarorin domin su tausa zuciyar shugabannin Hamas game da tsagaita wuta."

'Hamas na ɗaukar alhakin Falasɗinawa'

Mai sharhin yana ganin cewa wasu daga cikin abubuwan da ke faruwa bai kamata su faru ba idan shugabannin ƙungiyar Hamas suka ga dama, yana mai cewa ayyukansu ne ke jawo wa ana kashe fararen hula Falasɗinawa.

"Da ma Isra'ila ƙaramin dalili ta ke nema domin ta fara luguden wuta a kan Gaza," in ji masanin.

"Saboda haka, shugabannin ƙungiyar Hamas na ɗukar wani ɓangare mai girma na alhakin mutane da ake kashewa waɗanda ba su ji ba su gani ba, alhali su shugabannin suna wasu wurare a boye, wasu ma ba sa cikin ƙasar."

Tsagaita wuta zai yiwu kuwa? - Sharhin Paul Adams

Shin yaƙin da Isra'ila take wanda ake yi wa laƙabi da "Guardian of the Walls" ya kusa zuwa ƙarshe?

Amsar a bayyane take cewa a'a. Firaminista Benjamin Netanyahu ya ce hare-haren za su ci gaba "ba ƙaƙƙautawa" kuma "za su ɗauki lokaci."

Yayin wani taron manema labarai ranar Lahadi, ya yarda cewa ana matsa musu amma ya gode wa Shugaban Amurka Joe Biden musamman saboda goyon bayan da yake bai wa ƙasarsa.

Wakilin Mista Biden, Hady Amr, yana Isra'ila tun ranar Juma'a, inda yake tattaunawa da shugabannin ƙasar kan rikicin.

Tun da dama Amurka da wasu ƙasashe suna kallon Hamas a matsayin ƙungiyar ta'addanci, Mista Amr ba zai gana da shugabannin Hamas ba.

Duk wani saƙo da yake son bai wa Hamas sai dai ya aika shi ta hannun masu shiga tsakani - kamar Qatar da Masar.

Wasu rahotannin cikin gida na cewa Hamas ta fara neman a tsagaita a baya-bayan nan, wanda ita kuma Isra'ila ta ke yin watsi saboda tana son ta lahanta Hamas sosai kafin a kawo ƙarshen yaƙin.

Da ma wannan ba sabon abu ba ne: Isra'ila za ta yi ta amfani da ƙarfin soja har sai an yi kururuwa game da fararen hular da take kashewa da kuma rincaɓewar yanayi a birnin Gaza, abin da zai sa a ce to faɗan ya isa haka.

A wajen Isra'ila, wannan lokacin bai yi ba tukunna.