Vous-êtes ici: AccueilActualitésSanté2021 04 24Article 450413

BBC Hausa of Samedi, 24 Avril 2021

Source: BBC

Jiragen sojin Najeriya sun fatattaki mayaƙan Boko Haram a jihar Yobe

Wasu jiragen sama na sojojin Najeriya Wasu jiragen sama na sojojin Najeriya

Sojojin Najeriya da taimakon jirage masu saukar ungulu na rundunar sojin saman kasar, sun ce sun dakile wani harin 'yan kungiyar Boko Haram a garin Geidam da ke jihar Yobe.

Garin ne mahaifar sabon babban sifeton 'yan sandan Najeriya da aka nada wato Baba Alkali.

Wasu rahotanni sun ce mayakan na Boko Haram, sun mamaye Geidam a manyan motocin yaki, da zummar afka wa mutane yayin da suke shirin shan ruwa da yammacin jiya Juma'a.

Majiyoyi sun kuma ce sama da maharan goma aka kashe, sakamakon ruwan bama-bamai da jiragen soji suka yi musu.

Majiyar ta fada wa jaridar PRNigeria cewa duk da cewa sojojin kasa sun fatattaki wasu 'yan ta'adda da suka gudu bayan an dakile harin, amma babu tabbacin ainihin adadin wadanda aka kashe daga cikinsu.

Irin wannan lamarin ya faru a ranar Talata, 13 ga Afrilu, lokacin da sojojin Najeriya suka dakile hare-haren ta'addanci da yawa da aka yi niyyar kai wa sojoji da wasu Musulmai a lokacin buda bakin Azumin Ramadana, a Damasak da ke Jihar Borno.

Jaridar ta ce sojojin ƙsa na Najeriya, sun samu dauki daga jiragen sama na rundunar sojin saman Najeriya dake Damasak da Gajiram bayan da 'yan kungiyar ta Boko Haram suka far musu.

Wata majiyar leken asirin sojoji ta fada wa PRNigeria cewa 'yan ta'addar na kan hanyarsu ta daukar fansa ne don daukar fansar fitattun kwamandojinsu 13, wadanda sojoji suka kashe a yankin Tafkin Chadi a kwanakin baya.