Vous-êtes ici: AccueilActualitésSanté2021 05 17Article 450830

BBC Hausa of Monday, 17 May 2021

Source: BBC

Yadda yajin aikin kungiyar kwadago a Kaduna zai shafe ku

Yajin aiki a jihar Kaduna ya fara a ranar Lahadi kuma zai dawki tsawon kwana biyar Yajin aiki a jihar Kaduna ya fara a ranar Lahadi kuma zai dawki tsawon kwana biyar

A ranar Lahadi ne Ƙungiyar ƙwadago a Najeriya NLC ta kira yajin aiki a jihar Kaduna inda al'ummar jihar suka tsinci kansu cikin duhu - babu wutar lantarki saboda matakin.

Mahukuntan hukumar samar da hasken wutar lantarki a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya sun bi sahun yajin aikin inda suka nemi gwamnati da ta janye matakin da ta ɗauka na korar sama da ma'aikata 7,000.

Shugaban Ƙungiyar NLC a jihar, Kwamared Ayuba Magaji Sulaiman ya ce matakin da za su ɗauka shi ne durƙusar da harkoki a jihar daga ranar Lahadi har tsawon kwana biyar.

Rahotanni na cewa gwamnatin Nasir El Rufa'a ta ɗauki matakin rage yawan ma'aikatan jihar.

Gwamnatin ta ce ta ɗauki matakin ne saboda yawan kuɗaɗen da take kashewa duk wata wajen biyan albashi.

Amma shugabancin NLC a jihar ya yi fatali da matakin.

"Kawai gwamnati ta yanke hukuncin korar sama da ma'aikata 7,000 ba tare da sanarwa ba ko kuɗaɗen sallama," in ji Shugaban NLC.

"Mutane ne da iyalinsu suna da mutanen da suka dogara a kansu, don haka wannan matakin ba dai-dai ba ne.

"Wannan ne ya sa muka shiga yajin aiki sannan sauran kungiyoyin ƙwadago sun shirya don shiga yajin aikin har sai gwmanati ta soke matakin korar ma'aikatan."

Ƙungiyoyin ƙwadago ƙarƙashin NLC sun tura takarda ga ƙungiyoyin ma'aikata domin su shiga yajin aikin.

Yadda yajin aikin zai shafi jama'a

Kamfanin samar da wutar lantarki a Kaduna ya fitar da sanarwa inda ya sanar da abokanan hulɗarsa cewa za su fuskanci katsewar wutar lantarki saboda yajin aikin.

"Kamfanin rarraba hasken wutar lantarki ya amsa kiran NLC inda ya katse cibiyoyin ba da wutar lantarki mai karfin 33KV."

NLC ta kuma yi kira ga masu sana'ar babur da babur mai kafa uku su shiga yajin aikin.

Cikin takardar, kamfanin samar da wutar lantarki a Kaduna ya bukaci wadannan kungiyoyin su shiga yajin aikin:

  • Ƙungiyar ma'aikatan Samar da Abinci da Sigari


  • Ƙungiyar ma'aikatan ƙananan hukumomi ta Najeriya


  • Ƙungiyar ma'aikatan jinya da unguwar zoma ta Najeriya


  • Ƙungiyar ma'aikatan wutar lantarki ta Najeriya


  • Ƙungiyar ma'aikatan mai da iskar gas ta Najeriya


  • Ƙungiyar ma'aikatan gidajen rediyo da 'yan jaridu a Najeriya


  • Haɗaɗɗiyar ƙungiyar ma'aikatan gwamnati


  • Ƙungiyoyin ma'aikatan makarantu da ba malamai ba.


Me gwamnatin Kaduna ta ce game da yajin aikin?

Gwamnatin Kaduna ta gargaɗi NLC game da yajin aikin inda ta ce yajin aikin ya ci karo da dokar ƙwadago.

"Dokar ta kuma haramta ƙuntatawa duk wani mutum daga gudanar da harkokinsa saboda yajin aikin."

Sun kuma ce gwamnatin jihar Kaduna za ta kare dukkanin cibiyoyinta da kuma

ikon ma'aikata na shiga wuraren ayyukansu.

Ta kara da cewa dokokin kungiyar kwadago a Najeriya ba su lamunci rashin tsari ba,"

Mutane kuma sun shiga shafukan sada zumunta domin bayyana ra'ayinsu kan yajin aikin NLC a jihar.

Me El-Rufa'i ya ce?

Gwamnan jihar Kaduna ya mayar da martani ga wani sakon Tuwita da ke ikirarin cewa yajin aikin zai zama irin wanda ba a taba yi ba a jihar.

Sakon na cewa gwamnann a shirin kama shugaban kungiyar kwadago.

Gwamnan jihar Kaduna ya mayar da martani inda ya ce su ne iyayen munafukai kuma gwamnatinsa na nan tana jiransu.

Ga abin da wasu ke cewa

Sanata Shehu Sani ya ce rufe tashoshin jiragen kasa zai sa mutane su koma zirga-zirga kan titin da ya tashi daga Kaduna zuwa Abuja. "Gwara mutum ya jira a kammala yajin aikin."

Shi kuwa Dr Citadel cewa ya yi "lokacin yajin aikin sam bai yi ba, za a kara jefa rayuwar jama'a cikin mawuyacin hali."

Lehman ya ce "ya ce babu damuwa idan muka shiga wani hali amma idan a karshe matakin zai kawo farinciki a zukatan jama'a."

Aliyu Gana ya bayyana cewa masu ababen hawa sun yi tururuwa zuwa gidajen sayar da mai a Kaduna yayin da NUPENG ta bi sahun yajin aikin da Kungiyar NLC reshen Kaduna ta kira.