Vous-êtes ici: AccueilActualitésSanté2021 04 22Article 450365

BBC Hausa of Thursday, 22 April 2021

Source: BBC

Jihar Zamfara: 'Yan fashin daji sun kashe fiye da mutane 50

Wani ya shaida wa BBC cewa an kashe mutum 51 daga ƙauyukan gundumar Magami daban-daban Wani ya shaida wa BBC cewa an kashe mutum 51 daga ƙauyukan gundumar Magami daban-daban

Nan gaba a yau ne za a yi jana'izar ƙarin wasu mutane da 'yan fashin daji suka kashe jana'iza bayan wani mummunan artabun da ya yi sanadin mutuwar gomman mutane.

Wani shaida ya faɗa wa BBC cewa ya zuwa maryacen jiya Laraba, sun ƙirga mutum 51 da aka kashe daga ƙauyukan gundumar Magami daban-daban.

'Yan fashin daji sun auka wa mutane ne lokacin da suka yi yunƙurin kai ɗauki ga mutanen 'Yar Doka, waɗanda wasu bayanai ke cewa sun koma gida daga gudun hijira, kwana ɗaya kafin wannan ƙazamin hari.

Rahotanni sun ce har zuwa daren jiya mutane na ci gaba da tsere wa ƙauyukan yankin zuwa gudun hijira a Magami mai nisan kimanin kilomita 18.

Shaidu sun ce cikin mutanen da aka kashe akwai aƙalla mutum 20 daga ƙauyen Ruwan Dawa, sai goma na Kangon Fari Mana, shida daga Madaba, Arziƙin Ɗa ma mutum shida, Mai Kogo da Mai Aya-aya da Mai Rairai kowanne mutum biyu da Gidan Maza da Kunkelai mutum ɗai-ɗai.

Wannan shaida daga Kangon Fari Mana ya ce 'yan fashi sun shafe kimanin awa bakwai suna harbe-harbe

Bayanai sun ce mutanen ƙauyen 'Yar Doka da suka nemi ɗauki daga maƙwabtansu, sun koma gida ne kwana ɗaya kafin harin, don ganin ko akwai halin noma gonakinsu.

Sai dai a cewar mazaunan yankin 'yan fashin daji sun ci alwashin cewa ba za a yi noma ba a faɗin gundumar Magami, kuma suna tsammanin wannan ƙuduri ne ya sanya su yin gangami don sake auka wa ƙauyen 'Yar Doka.

A safiyar nan ne, ake jana'izar mutanen Kangon Fari Mana su goma a garin Magami.

Mutanen ƙauyen sun ce ba za su iya yi wa 'yan uwan nasu sutura ba a can saboda fargabar maharan za su dawo a kowanne lokaci.

Baya ga mutanen da aka kashe, wani shaida ya ce an kai mutum 11 da aka jikkata babban asibitin Magami inda suke ci gaba da samun kulawa.

Sun ce ba su da tabbaci ko an samu asarar jin rauni ko mutuwa a ɓangaren 'yan fashin daji, don kuwa sau da yawa sukan kwashi mutanensu ne su tafi da su.

Sun koka da rashin samun ɗaukin jami'an tsaro, waɗanda suka alaƙanta da lungun yankin nasu da kuma ƙarancin kayan aikin jami'an tsaro. Sun ce hatta jirgin yaƙin da ya je daga bisani bai iya fatattakar maharan ba.

A baya-bayan nan ne dai direbobin motoci da na baburan acaɓa a yankin musamman Ɗan Sadau sun gudanar da yajin aikin mako ɗaya don nuna wa mahukunta mawuyacin halin da suke ciki saboda ƙaruwar taɓarɓarewa tsaro, bayan harbe wani direba tare da sace 'yan matan amaryar da ya ɗauko a Mashayar Zaki, sai dai ga alama, har yanzu babu wani abu da ya canza.

Rundunar 'yan sandan jihar Zamfara ta ce ta samu rahoton kai hari a yankin, kuma an tura ƙarin jami'an tsaro. Don haka tana jiran su don jin tabbacin abin da ya faru a jiya Laraba.