Vous-êtes ici: AccueilActualitésSanté2021 04 26Article 450433

BBC Hausa of Monday, 26 April 2021

Source: BBC

Dangantakar Amurka da Turkiyya za ta kara tsami kan tarihin Armenia

Dangantakar Amurka da Turkiyya ta kara tsami kan tarihin Armenia Dangantakar Amurka da Turkiyya ta kara tsami kan tarihin Armenia

Gwamnatin Amurka na shirin yin wata sanarwa a yau Asabar dangane da abin da ake takaddama da shi a kai na cewa kisan kiyashi ne Turkawa na zamanin Daular Usmaniyya suka yi wa Armeniyawa a lokacin yakin duniya na farko.

Ana rade-radin cewa Shugaba Joe Biden zai ayyana daukar kisan a matsayin kisan-kiyashi, abin da Turkiyya ke musantawa, wanda hakan sauya matsaya ce ta dadaddiyar manufar Amurka, da kuma hakan zai kara tabarbara dangantaka tsakanin Amurkar da Turkiyya.

Tarihin abin da ya faru;

Kuasn kowa ya amince cewa dubban 'yan Armeniya ne suka mutu lokacin da Turkawa a lokacin Daular Usmaniyya (ta Turkiyya) suka kore su daga gabashin Anatolia zuwa hamadar Syria da sauran wurare a shekarar 1915-16, an kashe wasu wasu kuma sun mutu a sanadiyyar yunwa ko cutuka.

Shedu na kasashen waje da suka hada da 'yan jarida da jakadu da kuma masu wa'azin bushara sun bayar da rahoton wannan cin zali.

Akwai sabani kan ainahin yawan Armeniyawan da suka mutu, yayin da Armeniyawa ke cewa miliyan daya da rabi, kasar Turkiyya cewa take dubu dari uku ne.

Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ce ta bayar da sanarwar yin jawabin na kisan Armeniyawan karni daya da ya wuce, a hannun masu mulkin Daular Usmaniyya ta Turkiyya, a lokacin yakin duniya na farko.

Daman tun a lokacin yakin neman zabensa a shekarar da ta wuce, Shugaba Biden ya yi alkawarin amincewa da kisan Armeniyawan kusan miliyan daya da rabi a matsayin kisan-kiyashi, abin da har kullum hukumomin Turkiyya ke musantawa.

Tun a ranar Juma'a shugaban na Amurka ya yi magana ta waya da takwaransa na Turkiyya Recep Tayyip Erdogan kan batun.

A can kuma babban birnin kasar Armenia Yerevan, dubban jama'a ne suka yi tattaki a tituna a jajiberin taron shekara-shekara na tunawa da kisan.

Masu gangamin rike da wuta da kyandir da aka kunna, rike da tutocin kasar, sun rika cinna wa tutar kasar Tuurkiyya wuta. Wasu mutanen daga cikin masu gangamin sun ce abu ne da ke da muhimmanci a gare su, su tuna tarihinsu da kuma wadanda aka kashe;

Wani ya ce : ''Wannan ba abu ba ne da ake nufar wani mutum daya dan Turkiyya ba, abu ne a kan kasar Turkiyya, wadda ta gaza a manufarta, wadda ta tsara kisan-kiyashin kuma tsawon gomman shekaru tana yin duk abin da za ta iya domin batar da wannan kisan-kiyashi."

Wata mata cewa ta yi: ''Wannan abu ne mai muhimmanci sosai a garemu, muna bukatar adana wannan tarihi na tunawa da wadanda aka kashe, don kada hakan ta kara faruwa.

Duniya baki daya na son mu manta. Yahudawa ba su manta da kisan-kiyashin da aka yi musu ba, to saboda me mu za mu manta da kisan-kiyashin da aka yi mana?''

Wata kuma cewa ta yi: ''Ina ganin yanzu akwai dukkanin yanayi da Amurka za ta amince da faruwar abin, saboda musamman a lokacin wannan yaki, Armeniyawanmu sun nuna wa duniya gaba daya, idan ba kowa ya yarda cewa lalle an aikata kisan-kiyashi ba, to lalle hakan za ta iya sake faruwa. Dole ne dukkanin kasashe su yarda da haka, kuma su ce hakan ba za ta kara aukuwa ba''

Kasashen da suka amince kisan-kiyashi ne

Argentina da Brazil da Belgium da Canada da Faransa da Jamus da Italiya da Netherlands da Portugal da Rasha da Uruguay na daga cikin kasashe sama da 20 da a hukumance suka amince kisan kiyashi aka yi wa Armeniyawa. Sai dai wasu kasashen majalisun dokokin kasashen suka amince amma ba gwamnati ba.

Daya daga cikinsu fitacciya ita ce Amurka, wadda a 2019 majalisar dokokin kasar ta amince, abin da kasar Turkiyya ta yi kakkausar suka a kai.