Vous-êtes ici: AccueilActualitésSanté2021 05 15Article 450801

BBC Hausa of Saturday, 15 May 2021

Source: BBC

Yadda aka ceto yarinyar da aka kulle a keji tsawon wata takwas a Sokoto ba ci ba sha

Ƴan sanda sun ceto yarinyar ne mai shekara 12 da aka kulle a keji har tsawon wata takwas Ƴan sanda sun ceto yarinyar ne mai shekara 12 da aka kulle a keji har tsawon wata takwas

Rundunar ƴan sandan jihar Sokoto ta ceto wata yarinya da aka kulle har tsawon wata takwas.

Ƴan sanda sun ceto yarinyar ne mai shekara 12 da aka kulle a keji a ƙaramar hukumar Sokoto ta arewa.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar ASP Sanusi Abubakar ya ce a ranar Alhamis suka ceto yarinyar an kuma kama waɗanda suka kulle ta a gida.

Bayanai sun ce masu riƙon yarinyar ne suka kulle ta a ɗaki saboda rashin lafiyar da take fama da ita.

ASP Abubakar ya ce "an kulle yarinyar ne a keji ba tare da ba ta abinci ba na tsawon wata takwas.

"Lokacin da mutanenmu suka ɓalle kejin, yarinyar ta kasa tafiya saboda ta galabaita.

"Tana cikin mawuyacin hali, a cikin kejin take kashi da fitsari."

Ya ce yanzu sun ɗauke ta zuwa babban asibiti domin kula da lafiyarta

Ya kuma ce ƴan sanda za su ci gaba da gudanar da bincike tare da gabatar da waɗanda ake zargi.

A bara an ta samun irin wannan al'amari a Kano da sauran jihohin arewacin Najeriya inda ake kullewa ko ɗaure yara ƙanana.