Vous-êtes ici: AccueilOpinionsActualités2021 06 01Article 451084

BBC Hausa of Mardi, 1 Juin 2021

Source: BBC

UEFA ta fitar da fitattun 'yan wasa 23 a Champions League

Hukumar kwallon kafa Turai, Uefa ta bayyana 'yan wasa 23 da suka yi bajinta a gasar Champions League da aka kammala ranar Asabar.

Wadan nan 'yan kwallon za ta iya fuskantar kowacce kungiya da su daga kowacce nahiya da zarar an bukaci hakan.

Chelsea ce ta lashe kofin Champions League na kakar nan, bayan da ta doke Manchester City da ci 1-0 a Porto, Portugal.

Wannan shi ne karon farko da Thomas Tuchel ya lashe Champions League a tarihin sa na mai horar da tamaula.

Paris St Germain ce ta sallami kocin dan kasar Jamus a watan Janairu, ita kuwa Chelsea ta damka masa aikin koci, bayan da ta kori Frank Lampard.

Wannan shi ne karo na biyu da Chelsea ta lashe Champions League, bayan wanda ta dauka a 2011/12 ta kuma taba kai wa wasan karshe da Manchester United ta yi nasara a 2007/08.

Chelsea ta karkare kakar nan ta Premier League a mataki na hudu a kan teburi duk da rashin nasara da ta yi a wasan karshe a Villa Park.

Saboda haka Chelsea za ta buga gasar Champions League ta badi a matakin mai rike da kofi, kuma wadda ta yi ta hudu a Premier League ta kakar nan.

Haka kuma kungiyar Stamford Bridge za ta buga Uefa Super Cup da Villareal, wadda ta lashe Europa Cup a karon farko a tarihin kafa kungiyar shekara 98.

Villareal ta yi nasarar doke Manchester United da ci 11-10 a bugun fenariti, bayan da suka tashi wasan 1-1.

Wannan nasarar da Villareal ta yi ya sa za ta buga Champions League a badi kenan, kuma kungiyoyi biyar ne za su wakilci Sifaniya a gasar kenan.

Kungiyoyin sun hada da Atletico Madrid wadda ta lashe La Liga da Real Madrid ta biyu da Barcelona ta uku da Sevilla ta hudu a teburi da kuma Villareal mai Europa League na bana.

Za a buga Uefa Super Cup tsakanin Chelsea da Villareal cikin watan Agusta a Ireland ta Arewa.

'Yan kwallo 23 da Uefa ta bayya na Champions League:

Masu tsaron raga:

  • Thibaut Courtois (Real Madrid)

  • Ederson (Manchester City)

  • Edouard Mendy (Chelsea)


  • Masu tsaron baya:

  • Cesar Azpilicueta (Chelsea)

  • Rúben Dias (Man. City)

  • Marquinhos (Paris)

  • Antonio Rüdiger (Chelsea)

  • Ben Chilwell (Chelsea)

  • David Alaba (Bayern)


  • Masu buga tsakiya:

  • Jorginho (Chelsea)

  • Mason Mount (Chelsea)

  • N'Golo Kanté (Chelsea)

  • Kevin De Bruyne (Man. City)

  • İlkay Gündoğan (Man. City)

  • Luka Modrić (Real Madrid)

  • Sérgio Oliveira (Porto)

  • Phil Foden (Man. City)


  • Masu cin kwallaye:

  • Erling Haaland (Dortmund)

  • Kylian Mbappé (Paris)

  • Robert Lewandowski (Bayern)

  • Karim Benzema (Real Madrid)

  • Neymar (Paris)

  • Lionel Messi (Barcelona)