Vous-êtes ici: AccueilOpinionsActualités2021 05 01Article 450518

BBC Hausa of Saturday, 1 May 2021

Source: BBC

La Liga: Griezmann ya taimaka wa Barcelona ta kamo Real Madrid

Lionel Messi, dan wasan Barcelona Lionel Messi, dan wasan Barcelona

Barcelona ta yi nasarar doke Villareal da ci 2-1 a karawar mako na 32 a gasar La Liga da suka fafata ranar Lahadi.

Minti 26 da fara wasa ne Villareal ta ci kwallo ta hannun dan wasan tawagar Najeriya, Samuel Chukwueze.

Sai dai minti biyu tsakani Barcelona ta farke ta hannun Antoine Griezmann, sannan ya kara na biyu saura minti 10 su je hutu.

Villareal ta karasa fafatawar da yan wasa 10 a cikin filin, bayan da aka bai wa Manu Trigueros jan kati saura minti 25 a tashi daga gumurzun.

Da wannan sakamakon kungiyar ta Camp Nou tana ta uku a teburi ta hada maki 7i iri daya da wanda Real Madrid keda shi a teburin La Liga na bana.

Atletico Madrid ce ta daya da maki 73 mai wasa 32, sai Real Madrid ta biyu mai maki 71, ita kuwa Sevilla maki 67 tana ta hudu a kan teburin gasar Spaniyar.

A ranar ta Lahadi Atletico Madrid ke ziyartat Athletic de Bilbao a karashen wasannin mako na 33.

To sai dai Barcelona tana da kwantan wasa daya kenan da ya rage mata.