Vous-êtes ici: AccueilOpinionsActualités2021 03 19Article 449751

BBC Hausa of Friday, 19 March 2021

Source: BBC

Pogba ya kai Man United Quarter finals a Europa na bana

Pogba ya kai Man United Quarter finals a Europa na bana Pogba ya kai Man United Quarter finals a Europa na bana

Paul Pogba ya kai Manchester United wasan daf da na kusa da na karshe a Euopa League, bayan da ya ci Milan kwallo daya a San Siro ranar Alhamis.

Dan wasan tawagar Faransa ya yi wannan bajintar a mintu uku da aka sa shi wasa a zagaye na biyu a karawar. Wasan farko da suka yi a Old Trafford tashi suka yi 1-1.

Wannan ne wasan farko da dan kwallon mai shekara 28 ya buga wa kungiyar tamaula, bayan jinya a raunin da ya yi tun 6 ga watan Fabrairu.