Vous-êtes ici: AccueilOpinionsActualités2021 03 15Article 449659

BBC Hausa of Monday, 15 March 2021

Source: BBC

Kenya da Somaliya : Za a fara shari'a tsakanin ƙasashen kan rikici a kan iyakar teku

Shugaban Somaliya Mohamed Farmaajo da na Kenya Kenyatta (dama) Shugaban Somaliya Mohamed Farmaajo da na Kenya Kenyatta (dama)

Ranar Litinin ɗin nan ne ake sa ran kotun ƙasa da ƙasa ta Majalisar Ɗinkin Duniya za ta soma zaman shari'a tsakanin ƙasashen Kenya da Somaliya sanadiyyar taƙaddama kan iyakar teku dake tsakaninsu.

Sai dai wasu majiyoyin gwamnatin Kenya sun sanar da cewa ƙasar ba za ta halarci zaman shariar ba.

Ta kuma zargi kotun ta ƙasa da ƙasa da nuna son rai da kuma goyon baya ga wani ɓangare a shari'ar kan wani yanki mai girman gaske a kusurwar Tekun Indiya da ta ratsa yankin.

Taƙaddamar kan yankin mai ɗumbin arziƙin mai da iskar gas ta haifar da ricikin diflomasiyya tsakanin ƙasashen biyu maƙwabtan juna.

Tun da farko Kenya ta buƙaci a jinkirta sauraren ƙarar, yayin da take ƙoƙarin bai wa wata sabuwar tawagar lauyoyinta bayanin halin da ake ciki.

Bugu da ƙari ƙasar ta Kenya, ta kuma bayar da uzuri na annobar korona da ke kawo tarnaki ga lamura.

To sai dai a nata ɓangaren kotun ta bayyana cewa ya kamata a yi zaman sauraren ƙarar ta bidiyo a Litanin ɗin nan,.

Kenya, ta kuma nuna rashin amincewa da kasancewar wani alƙali dan ƙasar Somaliya a rukunin alƙalan da za su yi shari'ar kasancewar da ƙasarsa ake takaddamar.

A shekara ta 2014 ne dai Somaliya ta shigar da ƙara game da yankin da take takaddama a kai da kasar Kenya.

Ta ce kamata ya yi fasalin iyakar ruwa ya yi daidai da fasalin iyakar kan tudu, yayin da ita kuma Kenya ta ce a ko yaushe a kan dauki tsarin iyakar ne a mike, daga inda kasashen biyu suka hade a gabar ruwan.

An dai fahimci cewa ayarin lauyoyi kasar Kenya za su yi wa kotun bayani na minti 30 gabanin soma zaman shari'ar a hukumance.

Ita ma dai kasar Somalia na da wani korafi kan kasar ta Kenya, inda take zarginta da tsoma baki a harkokinta na cikin gida ta hanyar nuna goyon baya ga gwamnatin yankin Jubaland, wanda ke hamayya da gwamnatin tarayya ta kasar Somaliya.

To sai dai duk da wannan kumfar baki, kasashen biyu kawaye ne a game da yaki da mayakan kungiyar masu tayar da kayar baya ta Al-Shabbab wadda ke iko da wasu yankunan karkara na kasar Somaliya.

Kungiyar ta Al'shabbab na kai hare-hare da dama da suka janyo hasarar rayuka da dukiyoyi a kasar ta Kenya.