Vous-êtes ici: AccueilOpinionsActualités2021 04 01Article 449991

BBC Hausa of Thursday, 1 April 2021

Source: BBC

Me ya sa ake shan wahala wajen daƙile mayaƙan IS a Mozambique

Lardin Cabo Delgado a kasar Mozambique ne inda suke cin karensu ba babbaka Lardin Cabo Delgado a kasar Mozambique ne inda suke cin karensu ba babbaka

Mummunan harin baya-bayan nan da mayaka masu ikirarin jihadi kuma masu alaka da kungiyar (IS) mai da'awar kafa kasar Musulunci suka kai a arewacin kasar Mozambique ya girgiza kasashen duniya.

Daruruwan mayaka dauke da manyan makamai sun ci galabar mamye wani gari da ke kusa da katafariyar masana'antar sarrafa iskar gas ta kasar kuma mafi girma a Afirka.

Sun yi wa mutane da dama kisan gilla da suka hada da baki 'yan kasashen waje, da 'yan kasar mazauna yankin, inda suka bar sassan jikin gawawwakin mutane warwatse a kan tituna.

Ya aka yi hakan ta faru, kana me yasa gwamnatin Mozambique ta gaza wajen dakile ayyukan masu tayar da kayar baya, kana wane irin abu ne zai sa a iya cin galaba a kansu?

Su wanene masu tayar da kayar bayan?

Suna kiran kansu da suna al-Shabab da harshen Larabci da ke nufin ''matasa'' ko ''masu jini a jika''. Wannan akwai rikitarwa saboda ba su yi kama da ainihin kungiyar da ke da alaka da al Qaeda a kasar Somalia ba, da su ma ke kiran kansu da al Shabaab.

A maimakon haka, wannan kungiya a shekara ta 2019 ne ta yi mubaya'a ga kungiyar IS mai mazauni a kasashen Iraƙi da Syria, da ba sa ga-maciji da juna da al-Qaeda.

Sun kuma rada wa kansu suna Kungiyar Kasar Musulunci ta Lardin Tsakiyar Afirka (ISCAP), wanda har ila yau akwai rikitarwa saboda kasar Mozambique ba ta cikin yankin Tsakiyar Afirka.

A wani yanayi me maimaita kansa a wasu wurare a duniya, kamar kasashen Mali, da Iraƙi, da kuma Najeriya, wannan tayar da kayar baya ya kara fadada ne saboda yadda wasu bangarori ke kallon ana mayar da su saniyar ware a cikin al'amuran da gwamnatocin suke yi.

Lardin Cabo Delgado na kasar Mozambique inda suke cin karensu ba babbaka, yana da nisan kilomita fiye da 1,600 (mil 990) daga Maputo babban birnin kasar, amma kuma yana da arzikin masana'antar sarrafa iskar gas mafi girma a Afirka.

An kiyasta cewa masana'antar wacce kamfanin hakar danyen mai na kasar Faransa Total ke gudanar da aiki a wurin, darajarta ta kai dala biliyan 60 kwatankwacin fam biliyan 44, daga zuba jarin manyan kasashen duniya da suka hada da Birtaniya.

Mazauna yankin sun koka da cewa ba su ga alfanu ko kuma ci gajiyar arzikin a yankin su ba, wanda hakan ya fara haifar da hare-haren kungiyar masu tayar da kayar baya a shekarar 2017, wadanda daga bisani suka fadada zuwa kungiyar ''kasa da kasa'' bayan da suka samu goyon bayan kungiyar IS.

Mayakan wadanda ke sanye da tufafi a yamutse da kuma datti, da suka mamaye garin Palma a karshen makon da ya wuce na dauke da manyan makamai kamar su bindigogi masu cin dogon zango, da na harba gurneti.

Daga faifen bidiyon dakungiya IS ta saka a shafin yanar gizo aga bisani, kamanni daya da suke da shi ya nuna jan kyalle wanda da dama ke ɗaurawa a goshinsu.

"Duk da cewa tayar da kayar bayan a tsukun yankin ne,'' in ji Olivier Guitta, wani mai sharhi kan yanayin hadarin da ke tattare a yankunan siyasa da ke hukumar GlobalStrat kana ƙwararre a fannin ayyukan mayaka masu jihadi a kasashen Afirka, "al Shabaab ta nemi goyon baya daga kungiyoyi masu kaifin kishin Islama a yankin Gabashin Afirka.

''Shugabanni masu tsattauran ra'ayin addinin a can sun taimaka wa matasa da horo a fannin addini har ma da ayyukan soji a arewacin kasar Mozambique."

Don haka wannan ayyuka na 'yan tayar da kayar baya na yankin ne kawai da ya samu wata dama na kasancewa a karkashin inuwar kungiyar IS, ya kuma ja hankulan kaashen duniya ta hanyar munanan hare-hare da kashe-kashe kuma a kan muhimmin wuri a fannin tattalin aziki.

Wace hanya ce za a bi wajen samun galaba a kansu?

Daukar gagarumin mataki fiye da wanda ake dauka a yanzu ita ce amsar.

Bayan gano hakan a matsayin wata gagarumar matsala, gwamnatin Mozambique ta dauko hayar sojoji 200 masu bayar da''shawara'' daga kamfanin kwangilar daukar sojoji na Wagner Group mai zaman kan sana kasar Russia cikin watan Satumbar shekarar 2020.

Wadannan da akasari tsofafin dakarun sojin kasar Russia na musamman ne sun taba yin a kasashen Syria, da Libya, da wasu wuraren a bisa amincewar fadar Kremlin.

Sun kuma je da jirage marasa matuka da na'urorin nadar bayani, kamar yadda Olivier Guitta ya bayyana, amma kuma nasarar ba ta samu yadda suka yi tsammani ba.

"Bayan da suka sha gamuwa da jerin farmaki ta hanyar kofar-raggo kana aka bayar da rahoton mutuwar da dama a fafatawa daban-daban da aka yi a cikin katafaren dajin da ke gundumomin Cabo Delgado, sai da 'yan kwangilar sojojin na kasar ta Rasha suka sake koma wa sabon lale.''

Babbar matsalar ita ce rashin kwarin gwiwa daga bangaren dakarun tsaron kasar ta Mozambique da kuma rashin sanin abubuwan da ka je su zo daga bangaren shugabannin siyasar kasar.

Brigadier Ben Barry daga Cibiyar Horarwa a Fannin Harkokin Mulki (IISS) ya ce mayakan kungiyar IS sun nuna yadda iya fada a muhimman yankunan zai iya haifar da babban cikas ga gwamnati da abokan huɗɗarta.

"Samun galaba a yakin yankin birni na bukatar dakarun gwamnati su samu muhimmin horo a fannin dabarun yaki a cikin birane. Wannan na nuni da rashin kwarin gwuiwa na dakarun kasar Mozambique.

"Da alamu ba su samu taimako daga masu bayar da shawara a fannin ayyukan soji daga kasashen Yammacin duniya ba da kuma samun damar amfani da karfin soji ta sama, da manya makamai na zamani, da motoci masu sulke, duka masu muhimmanci da aka yi amfani da suwajen fatattakar dakarun IS daga kasashen Iraqi da birane da garuruwan kasar Syria."

A cikin kwanakin baya-bayan nan Cibiyar Tsaro ta Pentagon ta aike da aike da wasu dakaru masu sanye da korayen huluna masu horarwa don zaburar da yunkurin dakarun kasar ta Mozambique a kasar Portugals.

An bayar da rahoton cewa kasar Faransa na sa ido kan abubuwan da ke faruwa daga tsibirinta na Mayotte da ke kusa kana kasar Afirka ta Kudu na nuna goyon baya da makwabciyarta.

Amma kuma, duk wani yunkurin ayyukan soji daga manyan kasashen duniya na dauke da na shi barazanar.

"Kamar yada muke gani a wasu wurare a arewain Afirka,'' in ji Benjamin Petrini, wani mai bincike a cibiyar ta IISS, " girke sojoji masu yawa ka iya rura wutar rikicin tare da haifar da mtasaloli na karuwar tashe-tashen hankula.''

Amma ya kara da cewa '' taka rawar Afirka ta Kudu [wacce sojojinta suka kubutar da ma'aikata da dama da suka makale a farmakin baya-bayan nan] shi ma za a iya la'akari da shi.''

Dabarun yakin kungiyar IS masu muni da kuma ban tsoro ne.

Ba kamar al-Qaeda ba wacce duk da cewa ita ma kisa ta ke yi a irin ayyukanta, amma ta kan yi kokarin nemi goyon bayan mazauna yankin, su wadannan masu tayar da kayar bayan kan kaddamar da munanan hare-haren zub da jini a kan al'ummomin yankin, sukan rika yi musu yankan rago.

A wani farmaki cikin wannan shekarar ko da yaro mai shekara 11 bai tsira ba daga irin wannan ta'asa a kuma gaban .

A cikin lokaci kankane hakan ya haifar da fargabat, da kuma jefa tunanin cewa ba za a iya samun galaba a kansu ba.

Amma kuma ba da dadewa ba ayyukan masu tayar da kayar baya suka fara samun cigaba ba tare da taimakon 'yan gari ba.

Kungiyar Al-Qaeda a kasar Iraƙi ta tafka kuskure na gallaza wa al'ummar Musulmai 'yan Sunni farmaki a yankin Anbar a shekarar 2007 - kamar wajen datse yatsun mazaje a kan aikata karamin laifi na shan taba sigari - da ta hakan ne gamayyar dakarun da ke samun goyon bayan na Amurka a kasar suka juya wa kungiyar ta al-Qaeda baya a wani abu da aka fi sani da '' kan mage ya waye.

A kasar Mozambique zai iya kasancewa abu iri daya. Dakile ayyukan masu tayar da kayar baya ba wai nasarar sojoji ne ba kawai, ya hada da wata tsohuwar dabara ta ''neman amincewa da yardar mutane''.

Don haka, idan ana son samun galaba a kan wadannan 'yan tawaye, da farko yana bukatar samun karfin gwiwa a bangaren dakarun Mozambique da kuma taimakon kayan aiki daga kasashen waje.

Amma kuma kafin a samu nasara mai dorewa akwai bukatar daukar matakan da suka wuce hakan.

Yana bukatar shugabanci nagari da taimaka wa al'umomin yankunan; makarantu, da hanyoyi, da ayyukan yi - su wadatu ta yadda zai janyo hankulan mutane su ga cewa gwamnati ba ta mayar da su saniyar ware ba yayin da manyan kamfanonin kasashen waje ke zuke kwashe ma'adinai masu daraja da kuma arzikin kasarsu.

A kasar Afghanistan na ga yadda hannun agogo ya dawo baya a irin nasarorin soji a kan kungiyar Taliban da dakarun kungiyar tsaro ta NATO da na gwamnatin Afghanistan suka samu, saboda gazawar gwamnati.

Daga bisani yankunan da aka ƙwato daga mulkin kungiyar Taliban suka sake kubucewa bayan da dakarun suka fice kana 'yann sada da jami'an gwamnati suka sake dawowa kan halayyarsu ta cin hanci da rashawa da sauran abubuwan da ba su dace ba a kan al'mominsu.

Abin da zai iya faruwa a kasar Mozambique kenan muddin ba a bai wa sojojin da za su zo goyon baya ba wajen gyara al'amuran da suka shafi kyautata wa jama'a.

Idan da a ce

Da alamu mayaka masu jihadi na kasar ta Mozambique na yunkurin kafa tasu ''daular'' a lardin na Cabo Delgado province, kamar yadda kungiyar IS ta yi a birnin Mosul a shekarar 2014.

Babu alamun yiwuwar ko za su iya samun galabar karbe ikon katafariyar masana'antar sarrafa iskar gas ta dala biliyan 60.

Yayin da yake da matukar wahala a ce za su iya kula da ita da kuma fitar da iskar gas din waje, duk da haka zai ba su damar samun karfin tattalin arziki, ta hanyar samun kudaden tara kayan yaki da kuma tura wa kungiyar ta IS kudade a tsakiyar kasashen Iraqi da Syria.

Ya dauki tsawon shekaru biyar na mummunan artabun hadin gwiwar kasashe 83 kafin daga karshe a samu cin galaba kan mayakan daula da karshe ta kungiyar IS a kasar Syria.

Lokacin da aka kawo karshe, shugabannin manyan kasashen duniya sun ce dole ne a hanakungiyar IS sake kafa wata daula.

Muddin ba a ci galaba kan ayyukan masu tayar da kayar bayan kasar Mozambique ba, lallai wannan alwashi zai sha ruwa.